Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, inda ake fuskantar ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma zargin sayen ƙuri’u a wasu rumfunan zabe.
Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da NSCDC, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga tare da tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro. A garin Tsani, rahotanni sun nuna cewa mutum biyu kacal aka gani a rumfar zabe, yayin da aka hango motar sintiri da APC na jami’an tsaro.
- Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
A rumfar Birchi ta Kudu, inda aka yi rajistar masu zabe 808, kaɗan daga cikinsu ne suka bayyana, wasu kuma sun ce an basu ₦500 bayan sun kaɗa ƙuri’unsu. Duk da babu rahoton tashin hankali, ƙarancin fitowar masu zaɓe da zargin sayen ƙuri’u na ƙara haifar da shakku kan ingancin zaɓen.













