Masana’antar Nollywood tana gab da shaida wani gagarumin ci gaba, a yayin da Dakta Princess Ezinne Agwu, sabuwar mai shirya fina-finai a masana’antar Nollywood, ta kammala shirin fim na farko na miliyoyin nairori mai suna, “The Mandate,” a birnin Paris na kasar Faransa.
Dakta Ezinne, wacce ta canza sana’a daga mai shari’a ta kasa da kasa zuwa harkar fim, ta hada kai da fitaccen daraktan Nollywood, Ike Nnaebue domin kawo wannan wasan kwaikwayo a idon duniya.
- Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
- Ali Nuhu Ya Gabatar Da Lacca Kan Fina-finan Nijeriya A Faransa
Ike Nnaebue, wanda ya dawo harkar fina-finai na barkwanci bayan nasarar shirinsa na “No U-Turn,” shi ne darakta a wannan shiri wanda ake fatan idan an kammala shi ya zama irinsa na farko da wani dan Nijeriya ya taba shiryawa. Wannan fim din ya janyo wa Dakta Ezinne yabo mai yawa da suka hada da jinjinan ‘Jury Berlinale’ da kyaututtuka daga kwalejin fina-finan Afirka da bikin fina-finai na duniya na Durban.
Da yake magana game da fin din “The Mandate” da hadin gwiwarsa tare da Dakta Ezinne, Ike ya ce wannan buri ne na kowane mai shirya fina-finai, domin yin aiki mai nagarta tare da samar da fasaha mai muhimmanci.
Ya ce fim din “The Mandate” labari ne na jarumtaka a cikin duniyar da tsoro ya zama aikin yau da kullun.
Majiyoyin da ke kusa da ‘Royalty Life Studios’, inda Dakta Ezinne ke aiki a matsayin shugaba, sun nuna cewa kasafin kudin fim din ya wuce naira miliyan 700. Sai dai Dakta Ezinne ta ki tabbatar da ainihin alkaluman, inda ta ce, “Ba a gama fim din ba tukuna, za mu bayyana kasafin kudin fim din idan an kamala shi.
Labarin fim din ya nuna yadda Dakta Ezinne Egbuna, Darakta-Janar na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, wanda ke kalubalantar halin da ake ciki a fagen siyasar Nijeriya da maza suka mamaye.
A yunkurinta na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasar ci gaba, ta yi murabus daga mukaminta mai daraja ta tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar DPC, karkashin jagorancin Hon. Lucas Amadi, wanda yake fuskantar adawa mai zafi daga DPA da makiya na boye a cikin jam’iyyar tasa.
Fim din ya kunshi fitattun jaruman da suka hada da Femi Adebayo, Deyemi Okanlawon, Ali Nuhu, Kalu Ikeagwu, Okey Bakasi, Sarauniya Dimma Edochie, Chioma Nwoha da kuma gabatar da sabon jarumi, Peter Ngene.
Dakta Ezinne ta jaddada cewa shawarar da aka yanke na gudanar da ayyukan bayan fage a birnin Paris ya yi daidai da hangen nesanta na samar da labarun gida tare da jawo hankalin duniya.
Ta ce, “Mun himmatu wajen bayar da labarun gida ga masu sauraron duniya,” in ji ta.
Yayin wani taron manema labarai a Abuja za a sanar da cikakkun bayanai kan shirin fitar da fim din da kwanan wata.