Hukumar gudanarwar gasar Premier ta Ingila, ta ce ba zata sake dakatar da wasannin sabuwar kakar da aka shiga ba, saboda annobar coronabirus duk da cewa ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a fadin Birtaniya a ‘yan kwanakin nan.
Matakain hukumar kwallon kafar ta Ingila dai na zuwa ne a yayin da rahotanni suka ce, shugabannin kungiyoyin kwallon kafar dake gasar Premier sun soma tuntubar juna bisa nazarin tafiya hutun makwanni biyu cikin watan Janairu, domin dakile yaduwar annobar coronabirus, wadda kawo yanzu ta kama ‘yan wasa da kuma wasu jami’ai guda 18 cikin mako daya kamar yadda hukumar lafiya da take kula da gwada ‘yan wasan ta bayyana.
Sai dai wasu daga cikin masu horaswa a kungiyoyin dake Ingilan sun bayyana adawarsu da matakin tafiya hutun na makwanni biyu, ciki har da kocin Manchester United Ole Gunnar Solkjaer.
Yayin caccakar kudurin, Solksjaer ya ce babu abinda matakin dakatar da gasar Premier tsawon makwanni biyu zai haifar illa kara nauyi kan kungiyoyi domin kuwa ba shakka adadin wasannin da suke tunkara zai kara cushewa, bayan makamacin kalubalen da aka fuskanta, ya yin da aka dakatar da wasanni a zangon farkon da annobar coronabirus ta kai kololuwa.
A ranar Lahadi ne kociyan kungiyar kwallon kafa ta Westbrom Albion, Sam Allardyce ya bayar da shawarar sake dakatar da gasar saboda a cewarsa akwai mutanen da suke cikin firgici akan cutar saboda shekarunsu kuma suna cikin harkar kwallon kafar ta Ingila.
“Rayuwar wasu daga cikin mutane a harkar kwallon kafa tana cikin hadari saboda yadda cutar take yaduwa a wannan lokacin tabbas akwai bukatar ayi duba sannan aga yadda za’a bayar da hutun sati biyu domin aga yadda abubuwa zasu kasance” in ji Allardyce, wanda ya fara aiki da Westbrom a kwanan nan.
Ya kara da cewa “Ni yanzu babu abinda nake jira sai kawai cutar ta kamani saboda shekaruna sun shiga jerin wadanda cutar take wahalarwa hakan yasa nake ganin yakamata ayi wani abu akai saboda bani kadai bane akwai irina da yawa”
Shima kociyan kungiyar kwallon kafa ta Wolberhampton, Nuno Espirito, ya bayyana cewa idan har ana ganin bayar da hutun zai bayar da wata dama da za’a samu sauki yana goyon baya amma kuma tabbas kungiyoyi da ‘yan wasa sune zasu sha wahala idan aka koma.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Brighton Hobe Albion, Potter, ya bayyana cewa yana goyon bayan tafiya hutun domin rahoton da ake samu na bullar sabuwar nau’in cutar wanda kuma rahotanni suka bayyana cewa sabuwa ce kuma tana saurin kama mutane a yanzu sama da yadda cutar take a baya.
Sai dai Potter bai bayyana goyon bayansa ba na cewa akwai bukatar a tafi hutun duk da cewa wasu masu koyarwar suna ganin tafiya hutun zai bayar da dama wadanda suka kamu da cutar sun warke sannan kuma za’a samu saukin kamuwa da cutar.
Tuni dai sakamakon kamuwa da cutar da wasu ‘yan wasan sukayi aka dakatar da wasan da aka shirya bugawa a karshen satin daya gabata tsaanin kungiyouyin Eberton da Manchester City da kuma wasan Fulham da Tottenham da aka dage shima saboda yawan masu dauke da cutar a tsakanin ‘yan wasan kungiyoyin.
Sai dai tuni kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta koma daukar horo a filinta bayan da tun farko aka rufe filin daukar horon saboda yawan masu dauke da cutar a kungiyar kuma zasu iya buga wasansu na gaba a bikin sabuwar shekara.