Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta fitar da sanarwar tsaurara matakan tsaro a makarantu da asibitoci a daukacin kasar.
Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar ayyukan ta’addanci.
- NLC Ta Bukaci Buhari Ya Kara Albashin Ma’aikata Da Kashi 50
- An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 Na Birnin Beijing
Sanarwar da rundunar ta fitar a yau Lahadi, ta umarci dawo da shingen bincike da zai bayar da damar duba ababen hawa a lokacin da za su shiga gine-ginen gwamnati.
Sai dai shugaban ‘yan sandan ya umarce su da yi aikin cikin kwarewa ba tare da cin zarafin ‘yan kasa ba.
Wannan sabon matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ci gaba sa tunkarar babban zaben 2023.
Al’umma a Nijeriya da ma masu rajin kare su na martani a game da wannan mataki na dawo da shingen bincike, wanda suka ce duk da alkawarin da mahukuntan kasar suka yi na dawo da da’a a tsakanin jami’an ‘yan sanda har yanzu suna ci gaba da tsohuwar dabi’arsu wacce a shekarar 2020 ta jefa kasar cikin hargitsi har ta kai ga zanga-zangar ENDSars.
A baya-bayan matsalar tsaro na ci gaba da babbar barazana a Nijeriya, inda ‘yan ta’adda suka lashi takobin sace shugaban kasar, Muhammadu Buhari dungurugum.