Gwamnatin Tarayya ta lashi takobin sauya salon yaki da ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da kimiyyar zamani don magance matsalar tsaro.
Ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar wanda ya halarci taron bita ga malaman addinin Musulunci a ranar Talata, ya ce nasara kan yaki da ‘yan bindiga na da matukar wahala.
- Bai Kamata Jama’a Su Tsorata Da Bullar Zazzabin Lassa A Adamawa Ba – Kwamishinan Lafiya
- Alkaluman Sun Shaida Cewa Dole A Fahimci Ci Gaba Yayin Da Ake Kokarin Samar Da Shi
Maganar matsalar tsaro da tsadar rayuwa dai su ne manyan abubuwan da majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, ta jawo hankali a wajen taron, shi ya sa ministan ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ke dauka don murkushe matsalar baki daya.
Ya ce yanzu da zarar ‘yan bindiga sun fito kafin su gama kai hari su koma daji jami’an tsaro sun gama da su ta hanyar gano inda su ke da kuma daukar matakin tarwatsa su.
Ministan ya ce yana daga cikin salon yaki da ta’addanci wanda ya sa gwamnatin tarayya fara shirin kirkiro ‘yansandan jihohi.
Kazalika ya ce yanzu suna amfani da dabaru da na’urorin zamani wajen gano tare da dakile hare-haren ta’addancin ‘yan bindiga.