Tuni hukumar da ke tsara dokokin kwallon kafa ta duniya ta ce za a fara gwajin shudin-kati da dakatar da dan wasan da ya yi laifi na wani lokaci lokacin da ake tsaka da buga wasa.
Dan wasa zai kwashe minti 10 a wajen fili idan alkalin wasa ya ba shi shudin kati kuma tuni yanzu haka daman ana amfani ne da katina guda biyu – kati mai ruwan dorawa (Yellow card) a matsayin katin gargadi, da kuma jan kati (Red card) a matsayin katin kora.
- Wata Mata Ta Taba Zagina A Kan Littafina ‘Umarnin Uba’ —Yareema Shaheed
- Zargin Badakala: Emifiele Ya Sake Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Dala Miliyan 6
Har yanzu babu tabbas kan yaushe ne za a fara gwajin shudin katin da kuma gasar da za a fara yin gwajin amma tuni gasar Firimiya ta Ingila ta kawar da batun gwajin katin a wasanninta, yayin da Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta ce bai kamata a fara batun amfani da katin a manyan gasa na duniya ba a yanzu.
Hukumar tsara dokokin kwallon kafa ta duniya – wato International Football Association Board (IFAB) za ta gudanar da taronta na shekara-shekara cikin watan Maris a kasar Scotland, kuma batun shudin katin wanda a turance ake kira Sin-bin na cikin abin da za a tattauna.
Dama dai ana amfani da shudin kati a a wasannin kwallon kafa a mataki na kasa-kasa, amma ana sa ran kawo shi cikin manyan gasanni domin bai wa ‘yan wasan da suka yi mugunta.