Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfanin ƙasar China mai suna Kodong Manufacturing Nigeria Limited da zai riƙa harhada ababan hawa da suka hadar da motoci da babura masu aiki da batiri tare da samar da wuraren chajinsu a sassan jihar nan.
Da yake jawabi a yayin bikin sanya hannun, wanda aka gudanar a harabar kamfanin dake garin Dansudu a yankin karamar hukumar Tofa, Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya nanata ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin da zai karfafa gwuiwar masu zuba jari a jihar nan.
- Nijeriya Da Kasar China, Sun Sake Sabunta Yarjejeniyar Musayar Takardun Kudade Ta Naira Tiriliyan 3.28
- Shugaba Xi Ya Ba Da Umarnin Aiwatar Da Dukkanin Matakan Da Suka Wajaba Na Ceto Biyowa Bayan Girgizar Kasa A Xizang
Mataimakin Gwamnan na Kano ya ce a irin wannan yunkuri ne gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cire duk wani takunkumi daga bangaren gwamnati da ya dabaibaye harkokin kasuwanci a jihar nan.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce idan kamfanin ya fara aiki gadan-gadan, zai samar da guraben aiki na kai tsaye kimanin dubu biyu da samar da karin dimbin ayyukan yi da ba na kai tsaye ba tare da bunkasa tattalin arzikin yankin da jihar Kano baki daya.
Ya bukaci kamfanin da ya bayar da fifiko ga al’ummar garin Dansudu a yayin daukar ma’aikata manya da kanana.
Daga nan ya yi kira ga matasan da aka dauka aikin da ma wadanda za’a dauka su kasance masu gaskiya da amana tare da kiyayewa da kaidojin aiki.