ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsumman Jego

by Dausayin Musulunci
1 year ago
Annabawa

Allah Ubangiji tabaraka wata’ala ya bayyana kalaman Annabi Isah ga mahaifiyarsa yayin haihuwa: “fa nada ha man tahtiha alla tahzani kad ja’ala rabbuki tahtaki sariyya” Sai wanda ke karkashinta, ya kirata da cewa, karkiyi bakin ciki, lallai Ubangijinki ya sanya abinda ke kasanki ya zama farin ciki a gareki.

Wannan a bisa kira’ar wanda ya tafi cewa, Annabi Isah (AS) ya yi magana tun yana cikin tsumman jego sabida hujjar cewa, Ubangiji ya fada cikin Alkur’ani, ta bakin Annabi Isah tun yana tsummar jego da cewa, Ni bawan Allah ne, Ubangijina ya ba ni littafin dokokinsa kuma ya sanya ni na zama dan aikensa “kala inni Abdullahi ataniyal kitaba waja’alani nabiyya”.

  • LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
  • Kasar Sin Da Namibia Sun Sha Alwashin Daukaka Hadin Gwiwarsu Na Cin Moriyar Juna

Malamai sun ruwaito wasu daga cikin bayin Allah da Annabawa da suka yi magana tun suna tsumman jego.

ADVERTISEMENT

Annabi Muhammadu (SAW): An ruwaito daga Sayyada Amina tana cewa, lokacin da na haife shi, ya sauko yana Sujjada irin ta tsoho wanda ya dade a cikin addini yana bautar Allah yana fadi cewa bayan ya daga hannunsa da idanuwansa sama, na shaida babu wani Ubangiji sai Allah kuma ni ma’aikin Allah ne, “Ash Hadu Alla’ilaha’illallah wa ash hadau anni Rasulallah”

Bawan Allah Juraidu: Wani bawan Allah ne da wata mata ta yi masa sharrin zina, ta zo da dan jinjiri ta ce yaronsa ne, sai wannan bawan Allah ya umurci jinjirin da ya fada asalin mahaifinshi, take dan jariri ya bayyana cewa, mahaifinshi wani makiyayi ne a wuri kaza.

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

Akwai yaron da ya yi wa Annabi Yusuf shaida yayin da Zulaikha ta yi masa kagen cewa shi ne ya neme ta “Wa shahida shahidun min ahliha…”

Akwai wani sarki da ya rura wuta, ya ce duk wanda bai kafirta ba, to ya fada cikin wutar, akwai wata mata tana goye da dan jariri, ta zo fadawa sai ta tausaya wa jaririn ta tsaya, take jaririn yace Mama mu fada, mu ke da gaskiya, ba wuta ba ce Aljannah ce a gabanmu.

Akwai dan jaririn da ya yi wa wata bakar fata shaidar cewa ba ta yi zina ba, an jefe ta da yin zina sai wannan Jaririn ya kubutar da ita.

Akwai jaririn mashida, wata baiwar Allah ce da ta yi Imani da Annabi Musa, Fir’auna ya sa an yanka duka ‘ya’yanta a gabanta kan ta kafurta amma ta ki sai da aka zo kan dan jaririn sai tausayin shi ya kamata, sai dan jaririn ya ce Mama kina kan gaskiya kuma ki ci gaba da tsayawa kan gaskiya.

Mubarakul Yamama: wani yaro ne dan garin Yamama a garin Musailamatul Kazzabi wanda ya yi karyar Annabta, Manzon Allah (SAW) ya tambayi dan jaririn ne don ya tabbatar wa da mutanen garin cewa shi Annabin Allah ne da gaske ba irin nagarinsu ba makaryaci.

 Annabi Sulaiman (AS): Allah ya fada cikin hukuncinsa cewa, ya fahimtar da shi tun yana dan shekarun yarinta “Fa fahhamnaha Sulaiman…” an ruwaito cewa, ya warware wasu hukunce-hukunce masu sarkakiya tun yana dan yaro. Yana daga ciki, akwai wata Shari’a tsakanin wata kyakkyawar Mata da Mijinta na aure, sai Matar ta kai kara gun wani Alkali sai ya ce zai ba ta gaskiya amma sai ya yi lalata da ita, sai Matar ta ki amincewa, ta tafi wurin wani alkali, shi ma ya ce mata irin abin da na farko ya nema a wurinta, shi ma ta ki amincewa, har sai da ta je wurin alkalai hudu dukkansu suna neman abin da na farkon ya nema daga wurinta amma duk tana kin amincewa, sai Alkalan hudu suka jefe ta da sharrin zina! Sai aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar jifa, an kamo ta za a jefe ta sai Annabi Sulaiman (AS) ya gani ya tambaya abin da ya faru.

Take Annabi Sulaiman ya taro abokan sa yara ya shirya wasan kwaikwayo a gaban Babansa Sarki Dawuda, ya nuna duk irin abin da ya faru; ga wata an yanke mata hukuncin kisa za a jefe ta, ga shaidu Hudu, ga Sarki a kan kujera ga yaro a gefe ya ce, sarki hukuncin nan bai dace ta hakan ba; bayan an gama wasan kwaikwayo, Sarki Annabi Dawuda ya kira dan shi Annabi Sulaiman, ya ce dana, in kai ne ya za ka yi? Sai ya ce, dukkan shaidun hudu a yi musu tambaya irin abin da suka gani kuma kowa ya amsa tambayar ba tare da dayansa ya ji amsarsa ba, sai dukka shaidun suka bayar da amsa mabanbanta. Sakon Annabi Sulaiman ya isa. Matar ta kubuta, an jefe alkalan dukkansu Hudun a Shari’ar Annabi Dawuda.

Akwai kissar mata biyu da suka je daji suna wanke kayansu, kowacce tana da dan jariri, sai suka samu wani wuri suka kwantar da su, daga baya sai kura ta zo ta dauke dayan jaririn ta cinye, sai Matan suka fara takaddamma kowacce tana cewa, danta ne a raye. Sai suka kawo kara wurin Annabi Dawud, Annabi Dawud ya yanke hukunci ya bai wa wacce ba ita ce uwar dan ba, jaririnta ne kura ta cinye. Sai Annabi Sulaiman ya ce, Baba in ni ne ba haka zan yanke hukuncin ba, sai Annabi Sulaiman ya ce a nemo mai takobi ya raba jaririn biyu kowacce ta dauki daya, sai wacce ba jaririnta ba ne ta ce ta yarda, asalin uwar jaririn kuma ta ce ta hakura ta bai wa dayar jaririn.

Annabi Sulaiman ya ce wacce ta yarda a kashe jaririn ba ta san zafinshi ba don haka ba danta ba ne, wacce ba ta yarda ba, ta san zafinshi don haka a mayar mata da danta, nata ne. Imam dabrani, ya rawaito cewa, An baiwa Annabi Sulaiman alkalanta yana da shekaru 12 da haihuwa.

kissar Annabi Musa da Fir’auni yayin da ya cafke gemun sa tun yana dan karamin yaro, Fir’auna ya sa a kashe Annabi Musa sai Matarsa Asiya ta ce wannan yaro ne amma a jarraba shi da wuta da zinari.

Annabi Ibrahim (AS), Allah yana cewa mun shiryar da shi tun yana dan yaro “wa lakad a taina Ibrahim rushdahu min kablu…” yayin da aka haifi Annabi Ibrahim (AS), Allah ya turo masa Mala’ika ya sanar dashi Ubangijinshi a zuciya sannan kuma ya koya masa Zikiri a harshe.

Jarrabawar da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim da yanka dansa, an ruwaito cewa, Annabi Isma’il bai wuce shekara Bakwai ba a lokacin saukar umarnin amma ya ce Baba ka aiwatar da abin da Ubangiji ya hore ka.

Akwai tarihai na Annabawa da na bayin Allah da yawa da Ubangiji ya ba su hikima tun suna tsummar jego wasu kuma tun suna kan shekarun Yarinta.

Wannan ya nuna cewa, Annabawa Allah ya halicce su ne da kyawon halaye amma a bangaren Bayinsa akwai wadanda ake tsururinsu akwai wadanda kuma haka aka haife su da wadannan kyawon halayen. Kuma duk halayen da wani zai koya in aka hada su da na Annabawa, sai ka samu na Annabawa ya fi girma matuka.

In mutum halwa yake da kokarin yi, sai ka ji Allah yana cewa, Annabi Musa ya yi azumin kwana 40 safe da rana; Annabi Zakariya’u ya yi azumin kwana 3 a jere amma Annabi (SAW) ya ce Annabawa suna yin irin hakan ne ba don halayensu su karu ba, sai don godiyar Ubangiji.

Annabi (SAW) don ya tabbatar wa al’ummarsa cewa, dabi’un Annabawa da su ake haifarsu ba koya suke ba, dabi’ar dan Adam duk irin al’ummar da ya taso, irin halayyar wurin zai taso da ita, sai dai gaba in ya fada Duniya ya sauya, shi ya sa Allah ya ce, kowa a kan tafarkin Addini yake, sai daga baya iyayensa su sauya masa da wanda suke kai.

Annabawa
Dausayin Musulunci
+ postsBio
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Kyawawan Dabi’un Annabi Muhammadu (SAW)

MASU ALAKA

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City
Wasanni

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed
Labarai

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Next Post
Waiwayen Tsarin Hulda Da ƙasashen Waje Na Nijeriya A Matsayin Mafita

Waiwayen Tsarin Hulda Da ƙasashen Waje Na Nijeriya A Matsayin Mafita

LABARAI MASU NASABA

Ana Gudanar Da Taron Masana Ilmin Harkokin Kasar Sin Karo Na Uku

Ana Gudanar Da Taron Masana Ilmin Harkokin Kasar Sin Karo Na Uku

June 4, 2026
Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.