Yau Jumma’a 24 ga wata, aka yi bikin kaddamar da watsa shirye-shiryen talibijin na tashar Documentary ta CGTN da shirye-shiryen rediyo na tashar The Greater Bay na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG a Beijing da Hong Kong a sa’i guda.
Inda aka sanar da cewa, za a fara watsa shirye-shiryen CMG a Hong Kong kai tsaye a ranar 1 ga wata mai zuwa, a matsayin wata kyauta ta murnar cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, da kuma wani mataki na taimaka wa gudanar da manufar “kasar Sin, mai tsarin mulki biyu” a Hong Kong yadda ya kamata. (Kande Gao)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp