Samar da wadataccen abinci a jihar Oyo na fuskantar barazana saboda ayyukan Fulani Makiya a jihar, inda hakan ya juanyo akasarin manoma a jihar, musamman a karamar hukumar Ibarapa suka yi watsi da gonaknsu.
Har ila yau, manoman sun kuma yi watsi da sana’ar tas su saboda ayyukan hare-haren masu sace mutane domin karbar kudin fansa daga gun iyalansu da kuma ‘yan uwansu.
Bugu da kari akwai rahotanni da dama da aka wallafa kan yadda Fulani Makiyaya suka mamaye gonakan manoman inda suka cinye amfanin gonakan manoman, inda idan manoman sun tunkare su suke kashe manoman.
A lukuta da dama, manoman su kan kai rahoto ga jami’an tsaro a jihar domin su kawo masu dauki, amma duk hakan ya faskara.
A karamar hukumar Ibarapa a cikin jihar ta Oyo, ya kasance akwai dimbin manoma a yankin wanda kuma aka tabbatar da cewa, akasarin alummar a yankin, manoma ne wadanda suke bayar da gagarumar gudunmwar wajen samar da wadataccen abinci a jihar, amma kuma sai yankin ya kasance ana faman yin artabu tsakanin manoman dake a yankin da Fulani Makiya kuma hakan ya nuna a zahiri, babu ranar da za a iya kawo karshen matsalar.
A garin Igangan dake a cikin karamar hukumar ta Ibarapa ta Arewa, babu wata tantama karamar hukumar ce ta fi fuskantar matsalar yin garkuwa da mutane, fayde da sauransu.
Wata mata manomiya uwargida Elizabeth Eyinade ta bayyana wa jaridar Nigerian Tribune a yankin na Igangan cewa, Fulani Makiya sun jima suna takura masu, inda ta yi nuni da cewa, kuma mahukunta a jihar, musamman gwamnatin jihar bat a dauki wani matakin dakatar da hakan ba.
Elizabeth Eyinade ta ci gaba da cewa, “Idan muka yi shuka, Fulanin Makiyayan dake jihar suna hakikance da cewa, an kebe masu gurin ne domin yin kiwo.”
A cewar Elizabeth Eyinade, “Su na lalata mana amfanin gonar da muka shuka, idan kuma mun kai kara gun shugabansu, ya n ace mana ba abinda zai iya yi kan lamarin kuma basu da kudaden da za su iya biyan mu kan asarar da suka yi mana.”
Elizabeth Eyinade ta kara da cewa,“Fulanin Makiyayan bas a bamu damar mayar da hankulanmu domin yin noma mun kuma kai kararsu ga jami’an tsaro dake a jihar babu kirga wa, ama mai makon su dauki mataki, sai kawai su karbi cin hanci daga gun Fulanin Makiyaya su kashe maganar.”
Shi ma wani manomin a yankin Mista Tope Olabode ya sheda wa jaridar Nigerian Tribune cewa, Fulanin Makiyaya a jihar sun a mamaye masu gonakansu su lalata masu amfanin gonakansu sannan kuma su yiwa matan dake taimaka masu a gonanksu fyade.
Ya kara da cewa, iadan Fulanin Makiyayan suka lalata masu amfanin gonakan su, ‘yan sanda a jihar na karbar cin hanci daga gun Fulanin Makiyaya da suka kama sannan kuma su bayar da belinsu.
Shi ma wani manomi a yankin Igboora a karamar hukumar ta Ibarapa a jihar ta Oyo Wasiu Saalwu Agbaakin ya sanar da cewa, akwai lokacin da Fulani Makiyaya suka sare shi saboda ya yi fito na fito das us bayan sun mamaye gonarsa.
Wasiu Saalwu Agbaakin ya kara da cewa, akwai wani abokinsa manomi da shima Fulani Makiyayan suka sassare shi da wuka, inda har saran ya janyo masa matsala a hakarkarinsa.
Ya kara da cewa, “Mun kai shi Asibin kwararru na tarayya dake a garin Abeokuta, inda suka ki karbar shi sanna aka kai shi wani Asibitin kwarru dake a garin Ibadan, inda kuma bayan sati biyu muka maido dashi yankin na Igboora, inda daga karshe aka yi ma sa magani.”
Wasiu Saalwu Agbaakin ya kara da cewa, Fulani Makiyyaa sun kuma mamaye gonarsa day a shuka Shinkafa, Masara da kuma Rogo, inda ya ce, hakan ya janyo masa tabka asarar miliyoyin naira.
“Na samu nasarar kama Shanun Fulanin Mikiyayan guda biyu a gonar mahaifina day a shuka Kashu, inda na kulle su har sati biyu kafin in sake su zuwa ga masu su tare da bayar da gargadi kan kada a sake barinsu su shiga cikin gonakanmu.”
A karashe, manoman sun yi nuni da cewa, idan har ba a kawo karashen ayyukan na Fulani Makiyyaa a jihar ba, tabbas jihar za ta iya fuskantar barazar wadataccen abinci a wannan shekarar.