Cibiyar raya al’adu da rubuce-rubece da waƙn baka, Hausa International Book and Arts Festival (HIBAF), ta shirya gudanar da taron bajakoli karo na 5 a garin Kaduna, kamar yadda Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi ya bayyana.
Taron wanda aka fara gudanar da shi a shekarar 2021, na mayar da hankali wajen raya al’adun Hausa da suka ha5da da rubuce-rubuce musamman waɗanda aka yi a shekarun baya, da waƙen baka da kuma nuna wasu al’adu da aka manta ko kuma suke neman shuɗewa.
- Borno Ta Kashe Naira Biliyan 100 Kan Samar Da Tsaro A 2025 – Gwamna Zulum
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
Farfesa Malumfashi ya ce taron na bana zai mayar da hanakali ne wajen tattauna yadda ilimi addinin Musulunci ya yaɗu da adabi a ƙasar Hausa da kuma lokacin mulkin mallaka da kuma yadda tsarin ilimin yake a ƙasar Hausa, kuma taken taron na bana shi ne “Rumbunan Ilimi”
“A wannan karon za mu mayar da hankali kan yadda ake samar da ilimi da kuma yadda ake adana ilimin da aka samar da yadda ake zamanantar da shi”
Malumfashi ya ƙara da cewa; wannan zai faru ne ta hanyar samar da zaurarraaki da filaye da kuma damarmaki wajen tattauna yadda taken ko kuma mahangar jigon wannan taron na wannan shekarar zai kasance.
Za a gudanar da taron ne a ranakun 19 zuwa 21 ga watan Disamban 2025.














