Connect with us

WASANNI

Za A Gurfanar Da Shugaban PSG Da Tsohon Sakataren FIFA A Kotu

Published

on

Za a gurfanar da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain, Nasser Al-Khelaifi da tsohon sakatare janar na hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Jerome Valcke a watan Satumba kan zargin cin hanci da rashawa.
Ana zargin mutanen biyu da karbar na goro wajen bayar da damar tallata wasannin Fifa a kafar yada labarai bayan wani bincike da akayi kuma aka samu mutanen biyu da hannu acikin badakalar da ake zargi.
Akwai wani mutum na uku da ba a sanar da sunansa ba da ake zargi da yin shugabanci ta hanyar da ba ta dace ba da samar da takardu na jabu kuma shima zai shiga jerin wadanda za’a gurfanar din inda tuni aka yanke cewa za a saurari karar a garin Bellinzona, na kasar Switzerland.
Ana zargin Al-Khelaifi wanda ke kuma shugabantar rukunin kafar yada labarai ta BeIN, da laifin bayar da na goro ga Balcke domin a bai wa kamfaninsa damar tallata wasannin Fifa har da Gasar Kofin Duniya.
Sai dai kuma a watan Fabrairu ofishin mai shigar da kara a Switzerland wato atoni janar ya soke zargin da ake yi wa Al-Khelaifi na neman nuna gasar kofin tuniya ta shekara ta 2026 da ta 2030 a kafar yada labarai, bayan da suka cimma yarjejeniya.
Ana zargin Balcke da amfani da matsayinsa a hukumar kwallon kafa ta duniya tsakanin shekara ta 2013 da 2015 da tursasawa a bai wa Italiya da Girka damar nuna wasu Gasar Kofin Duniya a talabijin a wasannin shekara ta 2018 da na 2030, shi kuma ya amince da karbar na goro ta hannun wani attajiri.
Dukkan mutanen sun musanta zargin da ake yi musu sai dai kamar yadda wani rahoto daga kasar Faransa ya bayyana, zargin da ake musu yana da karfi kuma akwai hujjoji masu karfi da za’a iya kamasu da laifin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: