Majalisar wakilan Amurka ta zartar da muhimmin kudirin da ka iya haramta amfani da manhajar Tiktok a kasar.
Dokar za ta bai wa katafaren kamfanin sada zumunta na “ByteDance” mallakin kasar China, wa’adin watanni shida ya sayar da hannayen jarinsa ko kuma a toshe manhajar a fadin Amurka.
- Kasar Sin Na Kira Ga Amurka Ta Daina Danne Kamfanonin Waje Ba Bisa Adalci Ba
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
‘Yan majalisar sun jima suna nuna damuwa game da tasirin kasar China a kan manhajar ta TikTok.
Kamfanin kasar China Bytedance ne ya mallaki manhajar ta TikTok da aka kirkira a shekarar 2012.
An yi wa kamfanin mai mazauni a birnin Beijing rijista ne, a tsibirin Cayman, amma yana da ofisoshi a fadin nahiyar Turai da Amurka.
Idan har kudirin bai samu sahalewar Majalisar Dattawan Amurka ba, Shugaba Joe Biden ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen rattaba masa hannu da zarar ya iso kan teburinsa, abin da ake ganin na iya sabbaba takaddamar diflomasiya da kasar China.
Kamfanin Bytedance na bukatar samun sahalewar jami’an kasar China kafin kammala cefanar da hannayen jarinsa, matakin da mahukuntan birnin Beijing suka sha alwashin kalubalanta.
Akwai dokar tsaron China da ta bukaci kamfanonin kasar su yi musayar bayanai da gwamnati matukar aka bukaci hakan.
Manhajar ta TikTok ta yi kokarin bai wa hukumomin da ke sanya idanu a kan shafukan sada zumunta tabbacin cewar ta dauki matakan kare bayanan mutum milyan 150 da ke amfani da ita a Amurka daga ma’aikatan kamfanin Bytedance da ke kasar China.
Duk da cewar majalisar na da mambobi daga jam’iyyu guda biyu, an zartar da kudirin da kyakkyawan rinjaye, amma duk da haka sai ya samu sahalewar majalisar dattawa da sa hannun shugaban kasar kafin ya zama doka.