Hasashen hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet) ya nuna cewa wasu jihohin arewacin kasar daga ranar Litinin zuwa Laraba za su fuskanci yawan tsawa.
Hasashen NiMet da ta fitar a ranar Lahadi ya nuna cewa ana sa ran za a fuskanci hadari mai nauyi a yankin Arewaci inda ake sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe da Kaduna a safiyar Litinin.
“Daga bisani Kuma ana sa ran za a yi tsawa a sassan Arewa maso Yamma yayin da yankin Arewa maso Gabashin kasar nan shi kuma ya kubuta daga barazanar tsawar.”
Har ila yau, kiyasin hasashen ya nuna cewa “ana sa ran za ayi hadari mai karfi a yankin Arewa ta Tsakiya wanda hakan ya bada yiwuwar yin tsawa a sassan babban birnin tarayya, Filato, Nasarawa, Benuwai da Neja.
“Ana sa ran tsawa a sassan babban birnin tarayya, Kwara, Neja, Filato, Nasarawa, Benue, Kwara da Kogi a lokutan rana zuwa yamma.”