Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kammala shimfda layin doga daga Kano zuwa garin Maradi da ke cikin Jamhuriyar Nejar a 2025.
Wannan aikin dai zai lakume zunzurutun kudade wadanda suka kai dala biliyan 2, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da wannan kwangila.
- Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Tsara ‘Yan Nijeriya Da Farfaganda – Atiku
- Jami’an NSCDC Sun Cafke Matashin Da Ya Sace Babur Din Abokin Mahaifinsa
Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmad Alkali ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin da aka fara daga Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano wanda zai dangana har zuwa Maradi.
Ya ce aikin wanda aka rattaba hannu a shekarar 2021, ya nuna jin dadinsa game da yadda ake gudanar da aikin, yana mai cewa aikin ya kai kashi 80 cikin dari na kammalawa.
Ya ce, “Matakin aikin ya kai kashi 80 cikin 100 na kammalawa, yayin da aikin layin dogon zai fara aiki nan ba da jimawa ba bayan an kammala.”
Ministan ya kara da cewa, “Na gamsu da abin da muka gani. Mun zo ne tun daga Dawanau inda aka fara aikin domin mu samu bayanin matakin aiwatar da aikin, sannan kuma ‘yan kwangilar suka aiki daidai da matakin da aka diba wa aikin,” in ji Ministan.
Dangane da ko dan kwangilar zai iya cimma ranar da ake tsammanin kammala aikin, ministan ya bayyana cewa an yi manyan ayyuka, sannan akwai akwai duk wani hali da za a iya cimma buri.
Lokacin da ‘yan jarida suka tambayi ministan game da yuwuwar sake duba kudin aikin domin ya yi daidai da yadda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi a halin yanzu, sai ya ce, “Ina tunanin ko shi dan kwangila ya kamata ya yi sadaukarwa don bayar da gudunmawarsa na gyara Nijeriya da gwamnatin Tinubu ke jagoranta.”
A nasa bangaren, shugaban ‘yan kwangilan, Mista Bladislab Bystrenko, ya ce kudin kwangilar ya kai dala biliyan 1.95 kuma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar a shekara ta 2021 da gwamnatin tarayya.