Abdulrazak Yahuza Jere" />

Za A Koma Makarantu 18 Ga Janairu Amma Bisa Sharadi – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya

An samu kwarin gwiwa game da harkar ilimi a kasar nan, yayin da gwamnatin tarayya ta yi kwanare a kan matakin da ta so daukawa na hana komawa makaranta saboda annobar Korona da ta sake kunno kai a karo na biyu.

Gwamnatin tarayyar a yanzu ta amince makarantu su koma a ranar 18 ga watan Janairu kamar yadda aka tsara tun a karshen bara, bayan ta cimma matsaya da gwamnoni da kwamishinonin ilimi na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

An cimma matsayar ce a taron da ya gudana tsakanin Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da sauran kwamishinonin a Abuja.

 

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Mista Sonny Echono, wanda ya tabbatar da haka ga manema labaru, ya ce, “Mun tattauna sosai da gwamnoni, da masu makarantu, da ‘yan kwadago da wakilan kungiyoyin malamai da na dalibai. Kuma abin da muka cimma matsaya a kai shi ne mu sake bude dukkan makarantu.

“Sai dai kuma, wajibi ne a bi ka’idojin riga-kafin yaduwar Korona musamman wadanda aka gindaya da mutane za su rika yi su da kansu,” in ji shi.

Dalibai dai sun shiga damuwa sosai saboda yadda annobar Korona ta lalata musu tsarin karatu tun daga farko-farkon shekarar 2020.

 

Exit mobile version