Shugaban kungiyar alkalan wasa ta Najeriya (NRA), Sani Zubairu, ya mayar da martani game da rashin sunan alkalan Nijeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da za a yi a shekara mai zuwa a kasar Cote d’Ivoire.
Yana mai cewa suna kan tattaunawa da mahukunta domin magance matsalolin nan ba da dadewa ba.
- Super Eagles Ta Lallasa Saliyo Da Ci 3-2 A Gasar Zuwa AFCON 2023
- Babu Dan Nijeriya A Jerin Alkalan Wasan Da Za Su Jagoranci Gasar Kofin Afirka
A daren ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta fitar da jerin sunayen alkalan wasa 32 tare da mataimakan alkalan wasa 33, da jami’an VAR hudu,domin gudanar da kwas din shirye-shiryen AFCON na shekarar 2023, ba tare da alkalin wasan Najeriya ko daya a cikin jerin sunayen ba.
Sai dai kuma da yake mayar da martani,shugaban NRA ya ce kungiyar tare da hadin gwiwar hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) na kokarin ganin an shawo kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a saka alkalan wasan na Najeriya a gasar CAF da FIFA.
Zubairu, wanda ya zanta da LEADERSHIP ta wayar tarho, ya ce na yi bakin ciki kuma ban ji dadin hakan ba,amma wannan aiki ne na tarayya ba NRA kadai ba.
A iya sanina hukumar NFF ta yanzu karkashin jagorancin Ibrahim Gusau tana kokarin ganin an shawo kan matsalar da a koda yaushe ake yin watsi da alkalan wasanmu a gasar CAF da FIFA.
Tun da ya hau karagar mulki Ibrahim Gusau ya sha alwashin cewa zai tabbatar da an magance matsalar Zubairu ya shaida wa LEADERSHIP.
LEADERSHIP ta ruwaito alkalin wasa daya ne kawai dan Najeriya mai suna Samuel Pwadutakam aka zaba a matsayin mataimakin jami’i a gasar AFCON ta karshe a Kamaru daga cikin alkalan wasa 63 da suka jagoranci gasar.