CRI Hausa" />

Za A Yi Amfani Da Sabbin Fasahohi Da Dama Yayin Shagalin Bikin Bazarar Kasar Sin Na Shekarar 2021

Yau Lahadi, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya kira taron manema labarai game da shagalin bikin bazara na kasar Sin na shekarar 2021, inda aka yi cikakken bayani kan shirye-shirye masu ban sha’awa da sabbin fasahohin da za a yi amfani dasu yayin shagalin na wannan karo.

A yayin shagalin, za a maida hankali wajen nuna al’adun musamman na kasar Sin, da na kabilu daban daban na kasar, da kuma al’adu iri daban daban na kasa da kasa.
Haka kuma, domin magance yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, CMG zai yi amfani da wata sabuwar fasahar bidiyo wajen watsa shirye-shirye ga masu kallo a kasa da kasa.
Bugu da kari, a bana, CMG zai ci gaba da watsa shagalin bikin bazara ta yanar gizo a kasa da kasa. Kuma, kafofin watsa labarai sama da dari 6 a kasashe da yankuna sama da 170, da suka hada da kasashen Amurka, Faransa, Rasha, da kasar Indiya da sauransu, zasu watsa shirye-shiryen shagalin bikin bazarar kasar Sin kai tsaye, ko kuma gabatar da labaran dake shafar batun.(Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version