Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Za A Yi Wa Jami’an FSARS Gwajin Cutar Hauka

Published

on

Mataimakin shugaban ‘yan sanda ta qasa Joshak Habila ya gana da shuwagabanin rundunar ‘yan sandar SARS a shalkwatan rundunar ‘yan sanda. Ya yi amfani da wannan dama domin ya sanar wa shuwagabannin irin garanbawul tare da canca suna da za a yi wa ‘yan sandar FSARS. Habila shi ne shugaban kwamitin yin garanbawul wanda shugaban ‘yan sanda na qasa Idris Ibrahim ya kafa, an dai yi wannan ganawa ne ranar Asabar a Abuja, inda yake bayyana wa shugabanin irin yadda aikin zai gudana tare da jadda musu cewa dole kowani dan sandar SARS ya bi irin tsarin. Ya umarci shugaban ‘yan sandar SARS daya fara tilasta yin aikin da sabuwar dokan.
Shugaban sashin amsar qorafe-qorafen jama’a ta rundunar ‘yan sanda Abayomi Shogunle shi ne ya bayyana irin jerin abubuwan, cikin hadda gwajin cutar hauka da za a yi wa kowani dan sandar FSARS. Ya qara da cewa kwamitin FSARS zai siyarci dukkan rundunar SARS dake fadin qasar nan baki daya.
Ya ce “kwamitin garanbawul din zai gabatar wa rudunar ‘yan sandar SARS dake cikin qasar nan da sabon qudirin. Rudunar ‘yan sandar FSARS za su riqa kula ne kawai da laifuffukan irin na bashida makami da kuma laifin garkuwa da mutane.
“Kawai jami’ai masu kwazo ne za su inqa jakorantar rundunar FSAR. Duk wani jami’in da baya aiki yadda ya kamata to za a canza shi da wani. Yawancin jami’an FSARS za a kore su sakamakon rashin aiki yadda ya kamata.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: