Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Wudil da Garko a Majalisar Tarayya, Abdulhakeem Kamilu Ado, ya bayyana cewa za su ci gaba da ayyukan alheri domin ci gaban al’ummar da yake wakilta.Â
Mataimaki na musamman ga dan majalisae kan harkokin kafafan yada labarai, Musa Ali Karama ne, ya bayyana hakan.
- Gwamnan Jihar Filato Zai Garzaya Kotun Ƙoli Don Ƙalubalantar Hukuncin Soke Zaɓensa
- An Tsinci Gawar Mutum 9 Da Hatsarin Kwale-kwale Ya Rutsa Da Su A Jihar Neje – NSEMA
Ya ce dan majalisar ya yi wannan aiki ne da nufin Allah S.W.A ya kai ladan zuwa kabarin mahaifinsa Marigayi Hon. Kamilu Ado Ajiyan Makaman Kano, wanda ya rasu kwanaki shida kafin zaben 2023.
Aikin, wanda aka yi kwanaki uku ana yi an kammala ne a ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba 2023, inda aka yi wa kimanin sama da mutum dubu 1500.
La’akari da muhimmancin da ido yake da shi a jikin dan Adam ya sa dan majalisar ya dauki nauyin yin aikin kyauta a babban asibitin Wudil.
Kazalika, an yi wa al’ummar Karamar Hukumar Garko a asibitin cikin garin Garko, wanda aka kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanarwa.
Wasu daga cikin al’ummar da aka yi wa aikin sun amfana da gilashi da magunguna yayin da wasu kuma aka yi musu aikin tare da basu magunguna duk a kyauta.
Har ila yau, wasu daga cikin makwabtan kananan hukumomin Wudil da Garko su ma sun amfana da wannan tallafi, duk da ba ‘yan kananan hukumomin ba ne.
A karshe, Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado ya yi kira ga majinyatan da su kasance masu bin ka’idojin da likitoci suka gindaya musu don tabbatar da samun cikakkiyar lafiyar idanunsu, tare da fatan samun sauki