Gwamnatin Iran ta sanar da samun cikakkiyar nasara a gwajin sabon makami mai linzamin da ta yi, wanda ya yi tafiyar kilomita 2,000, ta kuma ce, za ta ci gaba da kera sabbin makaman, domin kara karfin sojinta, duk kuwa da matsin lamba daga Amurka na ta dakatar da hakan.
Sakamakon gwajin makamin na jiya Asabar, Amurka ita kadai, ta dauki matakin kakabawa Iran sabbin takunkuman karya tattalin arziki, bisa hujjar gwajin ya sabawa dokar da majalisar Dinkin Duniya ta gindaya, na haramta wa Iran din sake yin gwaje-gwajen makamai masu linzami, da ke da alaka da kera makamin nukiliya.
Cikin sakon da ya aike da shafinsa na Twitter, shugaban Amurka Donald Trump, cewa ya yi, gwajin da Iran ta yi, karara ya nuna raunin yarjejeniyar da tsohuwar gwamnatin Barrack Obama ya cimma da kasar a baya, kan dakatar da shirinta mai alaka da kokarin mallakar makamin nukiliya