Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Kylian Mbappe, ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar samun nasara a wasan da zasu kai ziyara kasar Jamus a sati mai zuwa a wasan cin kofin zakarun turai wasa na biyu.
Matashin dan wasa Kylian Mbappe ya zura kwallaye biyu a wasan da kungiyarsa ta Paris Saint German ta nuna bajinta har ta doke kungiyar kwallon kfa ta Bayern Munich mai rike da kofin da ci 3-2 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, matakin kusa dana kusa dana karshe.
kungiyoyin biyu, su ne suka fafata a wasan karshe na gasar a bara, amma Beyern Munich ce ta samu nasarar dage kofin a wancan lokaci wasan da har yanzu magoya baya da ‘yan wasan PSG suke tuna irin rashin nasarar da sukayi.
“Bayern Munchen babbar kungiya ce kowa yasan karfin kungiyar da ‘yan wasan da suke dasu da kuma tarihin da kungiyar take dashi a duniya da wannan gasa saboda haka sai mun dage a wasan mu na biyu” In ji Mbappe
Ya ci gaba da cewa “Amma muna da kwarin gwiwar cewa idan munje wasa na gaba zamu bawa duniya mamaki kuma zamu samu nasara kamar yadda muka samu a wasan da mukayi a ranar Laraba”
Kodayake masharhanta na cewa, rashin dan wasan gaba na Beyern Munich, Robert Lewandowski wanda ke jinyar rauni, ya taimaka wa PSG wajen samun nasara saboda Bayern Munich ta yi barin damarmakin zura kwallaye a raga har sau 31 wanda hakan yasa ake ganin idan akwai Lewandowski zai iya yin amfani da wasu daga cikin damarmakin da suka zubar din.
Kazalika alkaluma sun nuna cewa, kungiyar Bayern Munich ta fi rike kwallo da kashi 64, inda PSG ke da kashi 36 wanda hakan ya nuna yadda PSG din tasha wahala a wasan duk da kasancewar ta a gida take.
Bayern Munich ta buga wasanni har guda 19 a Gasar Zakarun Turai a jere ba tare da shan duka ba, amma PSG ta karya mata lago a ranar Laraba wanda hakan yasa ba zara karya tarihin Manchester United ba wadda ta buga wasanni 25 a gasar ba tare da yin rashin nasara ba.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta FC Porto ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 2-0 a matakin wasan na dab da na kusan karshe a gasar kuma nasarar da Chelsea ta samu ya rage mata radadin dukan-kawo wukan da West Brom ta yi mata da ci 5-2 a gida a gasar firimiyar Ingila a ranar Asabar din da ta gabata.
Matashin dan wasa Mason Mount da ya ci wa Chelsea kwallon farko a wasan, ya kafa tarihin zama dan wasa mafi karancin shekaru a Chelsea da ya zura kwallo a gasar zakarun Turai domin kuwa ya zura kwallon ne yana da shekaru 22 da kwanaki 87 da haihuwa.
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce, sun yi farin ciki amma ba sosai ba, ganin cewa, akwai haduwar da kungiyoyin biyu za su sake yi a ranar Talata mai zuwa, kuma komai na iya faruwa.
Za A Iya Dakatar Da Ibrahimovic Shekaru Uku
Tauraron kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, dan asalin kasar...