Connect with us

LABARAI

Za Mu Kammala Gyaran Matatu A 2023 – Kyari

Published

on

Kamfanin kula da harkokin mai na Nijeriya, NNPC, ya sanar da wata sabuwar ranar a tsakiyar shekarar 2023 da yake sa ran kammala gyara dukkanin matatun mai na kasar nan ta yanda za su iya gudanar da ayyukansu ka’in,da na’in.

Matatun mai na kasar nan da suke a Warri, Fatakwal da Kaduna, duk suna zaman banza ne a tsawon shekarun da suka gabata.
A cikin wani shirin talabijin wanda wakilinmu ya ganin ma idonsa ranar Lahadi da dare a Abuja, babban daraktan rukunin kamfanin man na kasa, Mele Kyari, ya kuma bayyana cewa a yanzun haka suna wani gagarumin shiri na mayar da matatun man cibiyoyin kasuwanci wadanda za su amfanar sosai.
Kyari yana yin wannan maganar ce a tare da karamin Minista a ma’aikatar albarkatun mai ta kasa, Timipre Sylba, a cikin wata tattauanawa da aka yi da su ta hanyar talabijin a cikin wani shiri.
Shugaban kamfanin ya ce, masu zuba jari masu zaman kansu za su yi aiki a tare da kamfanin domin gyara dukkanin matatun man, ya kara da cewa za a bi irin tsarin da aka bi a sashen samar da iskar Gas na kasar nan a kan matatun man.
“A wannan tsarin, kamfanin na NNPC zai kasance yana mallakan abu dan kadan ne a hadakar mallakar matatun man, in ji shi.
Kyari ya ce gaskiyar lamari, a yanzun haka matatun man zaman banza suke yi ba tare da suna aiwatar da aikin komai ba, amma ya yi nu ni da cewa, kamfanin man yana bakin kokarinsa wajen ganin ya farfado da su ta yanda za su rika tace wadataccen danyan mai a kasar nan.
A na shi bangaren, Sylba ya ce majalisun kasa a nan da ‘yan makwanni biyu ne za su fara yin aiki a kan sabuwar dokar sashen mai ta kasar nan.
Ya kuma bayyana fatar da yake da ita a kan sabuwar dokar, wacce ake ta jayayya a kanta tsawon shekaru ba tare da an iya tabbatar da it aba, wacce yake sa ran ta zama doka a karkashin wannan gwamnatin.
Ministan ya dage a kan cewa, sashen na man fetur an kasuwantar da shi, don haka farashin na tataccen man fetur kasuwar danyan mai ta Duniya ce za ta tantance shi.
Advertisement

labarai