Sabon mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro kuma tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu, ya kama aiki ranar Litinin, inda ya yi alkawarin samar da zaman lafiya a Nijeriya.
Nuhu Ribadu, wanda ya gaji Manjo-Janar Babagana Monguno bayan ayyana shi da shugaba Tinubu ya yi a ranar 19 ga watan Yuni ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro tare da samar da daidaito a Nijeriya.
- Amarya Da Kanwar Mijinta Sun Kubuta Daga Hannun Wadanda Suka Sace Su
- Dan Sanda Ya Shiga Hannu Kan Yunkurin Kashe Abokin Aikinsa A Kaduna
Wannan al’amari na zuwa a daidai lokacin da babban hafsan tsaron Nijeriya Manjo-Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa rundunar tsaron Nijeriya karkashin ikonsa za ta yi iya kokarinta na tattabar da maido da zaman lafiya a kasar nan.
Musa ya yi wadanan kalaman ne, a daidai sa’ilin da ma’aikatar tsaron kasar nan ta ke kokarin assasa wani ofishi da kuma ma’aikatar masana’antu na sojoji.
Ribadu, ya ce akwai gagarumin aiki a gaban gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da kasancewar Nijeriya kasa daya da kuma daidaita al’amura a kasar.
Mai ba da shawara kan lamurran tsaron kasar ya ce “wannan aikin ne da za’a yi wa ‘yan Nijeriya kuma manufarmu ita ce mu ci gaba da aikin da aka riga aka soma.”
“Za mu daidaita al’amuran kasar nan, za mu tsare kasar mu, kuma za mu samar da zaman lafiya a Nijeriya domin muna da yakinin cewa lokaci ya yi da kasarmu za ta ci moriyar zaman lafiya da dawo da doka da oda kamar yadda ya ke a sauran kasashen duniya” in ji shi.
Ya kara da cewa “tabbatar da ci gaba da dorewar a matsayin kasa wani abu ne da za mu ci gaba da aiki a kai. Za mu duba muga ayyukan da aka yi a baya sannan sai mu dora a kai. Domin cimma wannan manufa, za mu bukaci hadin kan ‘yan Nijeriya domin samun damar gudanar da ayukan mu kamar yadda ya kamata”.