Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, ya ce dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso zai kayar da abokan hamayyarsa da kuri’u miliyan uku a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamitin ga bayyana hakan ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da Cif Precious Elekima, Kodinetan Kudu Maso Kudu na kwamitin ya fitar.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Kare Hakkin Dan Adam Karo Na 38 Tsakanin Sin Da EU
- Wang Yi Ya Yi Kwarya Kwaryar Ganawa Da Antony Blinken Na Amurka
A cewar kwamitin, Rabi’u Kwankwaso zai yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya za su iya zabar shugabanni masu nagarta da kima.
Kwamitin na Kwankwaso ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa jam’iyyar za ta mara wa wani dan takara baya.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya nagari da su zabi mutumin da ya shahara da amana da gaskiya wanda zai ceto Nijeriya.
Ya kuma shawarci kafafen yada labarai da suke tantance labarai kafin wallafa su don gujewa tada labarun karya.