Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, za su yi tafiya da ministan Tinubu, Bosun Tijani wanda shi ne ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arziki na zamani, inda ya bayyana cewa zai ci gaba da rike mukaminsa bayan sun hambarar da gwamnatin Tinubu a 2027.
Da yake jawabi a ranar Laraba a wani bikin ‘Arewa Tech Fest’ karo na biyu a jihar Katsina, El-Rufai ya yaba da kwarewar Tijjani a fannin fasaha, don haka ya bayyana a fili karara cewa, ministan zai ci gaba da rike mukaminsa a karkashin sabuwar gwamnati, idan har hadakar da suke yi ta samu nasarar tsige shugaba Tinubu a 2027.
- Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa
- Tsaro Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙi – Atiku
“Za mu ci gaba da aiki da Bosun Tijjani saboda yana aiki mai kyau,” in ji El-Rufai yayin jawabinsa a wurin taron.
Arewa Tech Fest, taron koli ne na fasaha da kirkire-kirkire na kwanaki uku, wanda ke tattaro ’yan kasuwa, kwararru masu fasaha, masu zuba jari, da masu tsara manufofi don bunkasa fasahar kere-kere a Arewacin Nijeriya. El-Rufai ne da kansa ya shirya bikin.
Minista Tijani, wanda ya gabatar da jawabi mai mahimmanci, ya yi magana a kan sauye-sauye na zamani da kirkire-kirkire a sassan gwamnati da masu zaman kansu na Nijeriya.
El-Rufai ya isa wurin taron ne a makare, inda ya nemi afuwar mahalarta taron tare da bayyana cewa ya samu jinkiri saboda wani muhimmin taron siyasa da aka gudanar a yammacin jiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp