Hukumar kula da Inshorar kiwon lafiya ta jihar Kebbi (KECHEMA) ta dorawa kungiyoyin farar hula, kungiyoyin kwadago, kwararrun ma’aikatan lafiya da kuma kafafen yada labarai aikin bayar da shawarwari da yada labarai ga jama’a kan shirin Inshorar kiwon lafiya na hukumar a jihar.
Sakataren zartarwa na hukumar Dakta Jafar Augie ne ya bukaci hakan a wajen bikin rufe taron na kwanaki biyu da aka gudanar a Sukura Otal da ke jihar Sakkwato wanda aka shirya tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta Integrated Health Programme (IHP).
Ya ce, “Shirin na mu ne a matsayinmu na ’yan uwa da masu ruwa da tsaki a lokaci guda; ba na gwamnati ba ne, don haka ya rage gare mu na tabbatar da tsarin ya samun nasara ko akasin haka,’ Inji shi.
“Ya kamata mu rungumi tsarin mu mallake shi kamar yadda gwamnati ta yi aikinta ta hanyar ba wa tsarin doka da ka’idojin gudanar da aiki da kuma wuraren da suka dace.
“Babu abinci kyauta yanzu a duniya; dole ne mu ba da gudummawa don haɓaka ingantaccen isar da lafiya. Allah zai iya kalubalance mu idan muka zabi rashin tausayin jama’amu ga kula da kiwon lafiya,” inji shi.
Augie ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da dorewar da kuma tsayuwar tsarin Inshorar kiwon lafiya wajen samar da kudaden da za su bayar da gudummuwar cin nasarar tsarin, yana mai cewa alhakin ya rataya ne a kan dukkan masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, hukumar na da hurumin tabbatar da ingantacciyar hidimar kiwon lafiya ga kowa da kowa a jihar.
Haka zalika Dokta Augie ya yaba wa mahalarta taron, wadanda ya bayyana a matsayin, dukkan muhimman membobi na kungiyar aiki na fasaha kuma sun ba da himma wajen tsara tsarin.
“Za mu ci gaba da kasancewa masu godiya. Muna matukar godiya ga abokan aikinmu na ci gaba, USAID da hukumominta masu ba da tallafi ga kiwon lafiya da gudanar da mulki da Integrated Health Project (IHP) da sauransu,” in ji sakataren.
A nata bangaren, mai ba da shawara kan harkokin kudade da kasafi na IHP, Dakta Aisha Aminu-Senchi, ta bayyana cewa, IHP na hada kai da gwamnatocin jihohi wajen karfafawa da kuma ciyar da ayyukan inshorar lafiya na jihohi gaba, domin cimma burin samar da kiwon lafiya na duniya baki daya.
Ta bayyana cewa talakawan kasa ba za su iya biyan kudaden da samar da Inshorar lafiyar kansu ba, tana mai cewa ya kamata ’yan kasa masu wadata da su rika biyama wadanda ba su don amfani da kuma masu karamin karfi don iya dogaro da kai.