Za Mu Yi Iya Yinmu Wajen Doke Crystal Palace – Klopp

klopp

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce, yanzu hankalinsu ya karkata ga wasansu da kungiyar kwallon kafa kafa ta Crystal Palace ranar Lahadi wasan da zai tabbatar da gurbinsu a gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.
A wasannin baya-bayan nan dai Liverpool ta bayar da mamaki ta yadda ta koma matsayin na hudu a teburin daga ta 7 da ta ke a farkon watan nan, bayan nasararta kan West Brom a lahadin da ta gabata da kuma Burnley a ranar Alhamis, ko da ya ke har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin kuwa maki daya Liverpool din ta ke da Leicester City wadda ke matsayin ta biyar in banda tazarar yawan kwallaye.

Yanzu haka dai wasa daya ya ragewa dukkanin kungiyoyin na Firimiya 20 ya yinda kungiyoyin Chelsea da Liverpool da kuma Leicester ke cikin tsaka mai wuya domin kuwa dole daya daga cikinsu ta rasa gurbin na ‘yan hudu, bayan da Manchester City ta dage kofin ita kuma Manchester United ta bai wa kungiyoyin 3 gagarumar tazara.

Za’a iya cewa kai tsaye Liverpool ka iya samun gurbi a gasar ta cin kofin zakarun Turai bayan tagwayen nasarorin sai dai Jurgen Klopp ya ce lokacin fara murna bai zo ba domin kuwa sai har sun yi nasara da tarin kwallaye a haduwarsu da Crystal Palace ne za su iya kere Leicester City wadda taza fafata da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham.

Wasan na ranar Lahadi dai zai zama na farko da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta buga tare da magoya bayanta a filinta na Anfield tun bayan da aka dakatar da shiga fili saboda annobar cutar Korona.

Exit mobile version