Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Neja, ta sha alwashin sa kafar wando daya da ‘yan siyasa masu karfafa wa matasa gwiwar shan miyagun kwayoyi a lokutan yakin neman zabe.
Haruna Kwetishe, Kwamandan NLDEA na Jihar ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a yau Talata a Minna, cewa za a kama irin wadannan ‘yan siyasa tare da gurfanar da su a gaban kotu.
“Za mu sanya ido kan duk wani taron siyasa tare da kama duk wani shugaba da aka samu yana raba wa matasa miyagun kwayoyi a lokacin gangamin siyasa.
“Ba za mu lamunci duk wani nau’i na rigingimun siyasa da dabanci a lokacin yakin neman zabe da bayan yakin neman zabe ba.
“Za mu tabbatar da kamawa tare da gurfanar da duk wani mutum ko gungun mutanen da aka samu suna raba wa matasa miyagun kwayoyi a duk wani taron siyasa a Jihar nan,” a cewar kwamandan.
Ya ce rundunar za ta tura jami’an farin kaya zuwa wuraren yakin neman zabe domin sa ido da daukar matakan da suka dace a inda ya dace.
Kwetishe, ya ce rundunar ta hada kai da dukkan hukumomin tsaro domin magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a lokacin yakin neman zabe a jihar.
“Muna shirye-shiryen samar da yanayi na siyasa cikin lumana don aiwatar da duk harkokin zabe cikin lumana a jiharmu,” in ji shi.