Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Shugaban Majalisar Mahaddata Alkaur’ani na kasa, Gwani Aliyu Salihu Turaki, babban limamin Masallachin Juma’a na Alhassan dantata dake Kano, ya bayyana aniyar majalisar ta gudanar da saukokin Alkur’ani mai girma 1,111 a kowacce jiha domin rokon Allah ya kawo karshen barazanar matsalar tsaro da ke addabar kasarnan.
Shugaban na wannan jawabi ne jim kadan da kammala saukokin Alkur’ani 1,333 wanda aka gudanar a Masallachin juma’a na Shiekh Muhammadu Rabiu dake Goron Dutse a Jihar Kano ranar litinin data Gabata. Kamar yadda aka saba, wannan na cikin kokarin marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu Allah ya jikansa da gafara ke kokarin shiryawa wanda ya kira da ranar wannan taro da Yaumul-kur’an.
Gwani Aliyu Salihu Turaki ya bayyana cewa, babu wata mafita ga halin da ake ciki illa rungumar addu’o’i tare da yin tawassili da Alkur’ani domin rokon Allah kan halin da al’umma ke ciki. Saboda haka sai Shugaban ya bukaci shugabannin wannan Majalisa mai albarka na jihohin kasarnan da kowa ya shirya irin wannan taron addu’ar domin taimakawa aniyar Gwamnati na magance matsalar tsaro a fadin kasarnan.
Haka zalika Shugaban ya isar da Sakon bangajiya ga Alarammomi 1,111 da Suka halarci taron bana da aka gudanar a Gusau babban burnin Jihar Zamfara. Daga nan sai ya jinjinawa kokarin Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dr. Bello Muhammad Matawalle bisa hidimar da ya yiwa ahlullahi alokacin taron, ya yi addu’ar fatan Allah ya kawowa kasarnan karshen matsalar tsaro dake addabar kasarnan baki daya.
Taron na Yaumul-kur’an ya samu halartar Alarammomi daga kananan Hukumomin Jihar Kano 44, sai Kuma wakilin al’ummar karamar Hukumar birni dabkewaye Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, khalifa Alhaji Nafi’u Isyaka Rabiu da sauran manyan baki.