Connect with us

WASANNI

Za Mu Yi Wa Liverpool Tarbar Girma – Guardiola

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya ce ‘yan wasan kungiyar za su yi wa na Liverpool wacce ta lashe kofin gasar firimiya tarbar girma idan za su kara a filin wasa na Etihad ranar Alhamis.

Wasan shi ne wasan farko da Liverpool za ta buga a firimiyar Ingila, tun bayan da ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 30 kuma Liverpool ta ci kofin bana saura wasanni bakwai-bakawi a karkare kakar bana da tazarar maki 23 tsakaninta da Manchester City wadda take a mataki na biyu.

Kuma nasarar da Chelsea tayi na doke Manchester City da ci 2-1 a gasar firimiyar a filin wasa na Stamford Bridge itace  tasa kungiyar wadda mai koyarwa Jurgen Klopp ke jagoranta ta zama zakara a shekarar nan.

“Za mu yi wa Liverpool tarbar girma da zarar sun zo filin wasan mu na Etihad buga wasan firimiya saboda sun cancanta da muyi musu wannan tarbar girmar sakamakon bajintar da suka nuna tun farkon fara gasar ta bana,” in ji kocin Manchester City, Guardiola.

Ya ci gaba da cewa “Za mu gaisa da Liverpool da zarar sun zo gidanmu kuma ta kayatatciyar hanya sannan za mu yi haka ne ba don komai ba sai dai domin sun cancanta mu basu irin wannan girma.”

Sai dai kuma Guardiola bai ce komai ba kan tambayar da aka yi masa ko zai tsawaita zamansa a Manchester City, bayan da yarjejeniyarsa zata kare a karshen kakar wasa ta shekara ta 2021 kamar yadda ya kulla yarjejeniya tun farko.

A lokacin zai cika shekara biyar yana jan ragamar Manchester City, fiye da shekarun da ya yi a Barcelona sai dai tuni ake cewa Guardiola na son gwada sa’a a wata kungiyar, musamman idan aka tabbatar da hukuncin dakatar da kungiyar kaka biyu daga shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: