Zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun a majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Madami Garba Madami, ya rasu.
Ya rasu ne da safiyar ranar Asabar sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana ta ba a wani asibitin Kaduna.
- Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda 6 Da Kwato Makamai Da Dama A Kaduna
- Hukumar Jiragen Kasa Ta Dawo Da Aikin Jigilar Fisinjojinta Daga Abuja Zuwa Kaduna
Duk da cewa zababben dan majalisar ya karbi takardar shedar sake komawa kan kujerarsa daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bayan kammala babban zabe amma bai samu damar halartar taron kaddamar da zauren majalisar dokokin jihar ba a ranar 13 ga watan Yunin 2023, sakamakon rashin lafiyar da ta yi sanadin mutuwarsa.
Marigayi Madami ya taba zama shugaban karamar hukumar Chikun kuma tsohon kwamishina a jihar kafin ya tsaya takara inda ya kayar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun a zaben majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023 a karkashin jam’iyyar PDP.