Zababben Kansila Mai Wakiltar Al’ummar Unguwar Garba Daho, a karkashin Jamiyya mai mulki APC, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Karamar Hukumar wanda ke fadar Gwamnatin Jihar Filato, HONARABUL AUWALU LADAN GARBA.
A makon da ya gabata ya tattauna da wakilimmu da ke Jos Lawal Umar Tilde a kan gunagunin da wadansu suke yi a kan jamiyyarsu ta APC, ta tsaida Musulumi mataimakin dan takar Shugaban Kasa Cif Bola Tinibu, (wato muslumi da musulmi), a zabe mai zuwa na 2023, da irin darussan da ya koya a cikin ‘yan watannin da ya yi a ofis da fara jagorancin al’ummar mazabarsa da nasarorin da ya samu ya zuwa yanzu da sauran batutuwa bisa yanayin da kasar ke ciki, ga yadda hirar tasu ta gudana.
- Gwamna Buni Ya Cika Alkawarin Saya Wa Iyalan Sheikh Goni Aisami Gidaje
- Gwamna Buni Ya Cika Alkawarin Saya Wa Iyalan Sheikh Goni Aisami Gidaje
Honarabul ko zaka gabatar mana da kanka?
Bismillahi rahamanirrahim, Wa Sallallahu Alannabiyil Karimi, suna na Honarabul Auwalu Ladan Garba, Mataimkin Kakakin Majalisar Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alummar wannan Unguwa ta Garba Daho, sun zabe ka ka wakilce su a majalisar Karamar Hukumar Jos ta Arewa, ya zuwa yanzu wadanne darussa ka koya a wakilcin da kake yi wa mutanen wannan Unguwa? Alhamdu Lillahi, kasancewar ina wakiltar dubban daruruwan mutane, a nan Karamar Hukumar Jos ta Arewa da take fadar Gwamnatin Jihar Filato, babu shakka na koyi darussa masu yawa domin mutane kowa da irin nasa tunanin, to ka ga sai mutum ya sami cikakkiyar nutsuwa zai cimma nasarar biya wa mutane bukatunsu.
To wadanne irin kalubale ka fuskanta cikin dan wannan lokaci da ka fara jagorancin al’ummar wannan mazaba taka?
Kamar yadda kowa ya sani yanzu ana cikin wani mawuyacin hali na tsadar rayuwa bama a Nijeriya kawai ba a duk Duniya, mutane za su zo maka da damuwa iri-iri, don kai ka fi kusa da gwamnati, wannan yana daya daga cikin kalubalen da na fuskanta kuma yake bani tausayi.
To yanzu mene ne burinka na ganin ka bar wani abin tarihi a mazabarka?
Daga cikin burace-buracena, don suna da yawa, ina kuma godiya wa Allah domin na fara wadansu, na sami nasarar horar da matasa jimillar 280 an koya masu sana’o’i har mun yi bikin yaye su, kuma na sami dinka Unifon din makaranta don rarraba wa wadanda ba su da shi a makarantun da ke a mazaba ta kuma na saya wa matasa masu sha’awar buga kwallo kayan wasa, kuma ina kokari ganin na taimaka ta wajen addini amma babban burina shi ne in ga wannan mazaba ta sami Asibitin Gwamnati domin ba ta da shi wanda take da shi din mutanen unguwa ne suka hada sisi da taro suka fara ginin, sannan wani bawan Allah Alhaji Abubakar Sadik Fluza, ya zo ya karasa ginin kuma ake amfani da shi a yanzu. To ina son kafin na bar ofis in da gwamnati ta zo ta gina mana Clinic a wannan mazaba.
A matsayinku na masu aiwatar da dokoki da ba da shawara ga majalisar zartarwa na karamar hukuma, ban sani ba ya zuwa yanzu ko kun sami zartar da wadansu dokoki?
Bamu sami mun yi doka ba, sai dai akwai ayyukan da muka aiwatar da su da dama suna daga cikin ayyukan da ke gabammu na cewa za mu yi dokoki kuma za mu ziyarci wuraren sana’o’in mutane da kasuwanni don ba da shawara fa majalisar zartarwa yadda za a sami karin kudaden ci ga wa asusun karamar hukuma da kuma ziyartar unguwanni don mun sami koke-koken mutane mu ba da shawara yadda za a sami damar warware su kuma Alhamdu Lillahi mun sami nasara.
Ma za ka ce game da dokar bai wa kana’nan hukumomi cin gashin kansu wanda har yanzu ake kai ruwa rana a kanta?
To idan muka waiwaya baya za mu ga ai lokacin da Obasanjo yake a kan mulki Gwamnonin jihohi suka nemi a yi wani asusu na hadin gwiwa daga nan abubuwa suka tabarbare, tun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya hau karagar mulkin kasar nan yake ta kokarin yin gyara a kan dokar da za ta bai wa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu wanda wannan idan aka samu Buhari ya yi nasara a kan mayar da dokar zai cire talakan kasar akan kangin talauci da suka sami kansu ciki domin kana’nan hukumomi sun fi kusa da talakawa, karamar hukuma ta kan iya samar wa dubban daruruwan mutane ayyukan yi sannan kuma za ta yi ta gudanar da ayyukanta kai tsaye wanda za ka ga arziki na saurin shiga hannun mutane muna fata shugaban kasa zai cimma wannan buri nasa kuma ina kira ga al’ummar kasar nan da su taya majalisun kananan hukumomi da addu’a, sossai wannan yunkuri Allah ya sa a cimma nasara a mayar wa kananan hukumomi da dokar ikon cin ga cin kansu, domin yanzu asusun kananan nan hukumomi ya zama wa gwamnoni tamkar katin ATM, da su ke ta zukar kudin kananan hukumomi yanda suke so, su yi abin da suke so da su ba mai ce masu uffan. Maimakon su bar wadannan kudaden su je wa kananan hukumomi kaitsaye, da yardar Allah idan mutane suka bai wa kudurin goyon baya kafin saukar Shurgaban Kasa Muhammadu Buhari, daga mulki a shekara mai zuwa zai cimma nasara ya sanya hannu a kan dokar ta fara aiki.
Ma za ka ce game da sukar da gwamnatinku ta APC, take samu bisa tsaida mataimakin shugaban kasa a tsarin musulmi wato idan Allah ya sa jamiyyar ta kafa gwamnati za a yi shugaban kasa Musulmi mataimakinsa Musulmi?
Wato mutane suna da saurin mantuwa ne domin an taba yin haka a baya ba sau daya ba, idan za ka iya tunawa a lokacin General Gowon, ya mulki kasar nan na tsawon shekar Tara, ai mataimkinsa Kiristane a tsawon shekaru Tara da ya yi yana mulkar kasar, amma ba wanda ya ce uffan, kuma ya jagoranci kasar cikin nasara haka kuma a lokacin da marigayi M K O Abiola, ya nemi takarar shugabancin kasar ai ya dauki Musulmi Baba-Gana Kiggibe, ya zama masa mataimaki, kuma ba a taba yin karbabben zabe kamarsa ba a kasar nan Allah ne kawai ya sa ba zai jagoranci kasar ba, idan Allah ya yarda jam-iyyarmu ta APC, ita ce za ta lashe zabe domin dan takararta ya yi an gani a lokacin da ya zama Gwamna a Lagas ya gudanarda ayyuka wadanda suka daga darajar jihar ta zama zakara ta fuskar cigaba a tsakanin jihohin kasar nan.
Game da matsalar tsaro da ya addabi kasar nan musamman a jihohin Arewa, wace hanya ce mafita a ganinka?
Shi wannan matsala na rashin tsaro ya samo a sali ne daga faduwar gwamnatin Mu’ammar Gaddafi na kasar Libiya, wannan ya sa kasashen da suke kudancin Libiya suka sami kansu a cikin wannan matsala ta rashin tsaro saboda yaduwar makamai da ake safaransu daga Turai, ta kasar zuwa kasashen Africa dake nahiyar Kudancin kasar. Mutane suna kuskure bisa dora wa gwamnati kawai kan ta addanci a kasar nan dole sai an tube an tashi an taimaki gwamnati za a cimma nasara wajen yakar wadannan yan ta’adda kuma ina kira ga al’ummar kasar nan da su ci gaba da yin addu’a, kuma manta da bance-bancen addini da na siyasa su hada kai da gwamnati wajen yaki da yan ta adda kasar nan don sami cigaba ta fuskar inganta tattalin arzikinta da shimfidan dawwammiyar Dimukrdiyya a kasar.