Shugaban hadaddiyar kungiyar manoma ta Nijeriya(AFAN) reshen jihar Kano Alhaji Faruo Rabi’u, ya bayyana cewa zaben da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Muhammad Sabo Nanono daga jiahar Kano a matsayin minstan gona zabe ne wanda ya cancanta kuma kasancewarsa hamsakin manoni mai kuma kishin al’ummar kasar nan ta ci gaba, zai habaka harkar noma a Nijeriya.
Fauk ya fadi hakan ne a wajen liyafar da hadaddiyar kungiyar manoman reshen jihar Kano ta shiryawa ministan gonan domin taya shi murna da kuma yi masa fatan alheri tare kuma da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa cika kwana dari da ya yi a wannan zangon na biyu.
Sannan ya ci gaba da cewa, suna da tabbacin cewa, ministan zai taka rawar gani sosai a harkar noma a wannan kasa domin shi manomi ne, ya san dukkan matsalolin da manoma ke fama da su, sannan kuma shi tsohon dan hadaddiyar kungiyar manoma ne, nan ma ya san matsalolin kungiyar manoma, saboda haka zai yi dukkan abin da ya dace wajen ganin ya taimaka wa dukkan kungiyoyin manoma yadda za su samu ci wajen gudanar da sana’ar ta su ta noma.
Faruk ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wannan karramawa da ya yi wa al’ummar jihar Kano, ta bai wa dan jihar wannan matsayi na ministan gona, wanda al’umma za su amfana da kwarewar da yake da ita a wannan fanni.
Ya ce, Sabo Nanono mutum wanda wanda Allah ya azurta shi da bai wa ta iya hulda da jama’ da kuma kyakkyawan tunanin yadda za a samu ci gaba. Saboda haka shugaban ya ce, suna tabbacin cewa, ministan zai bayar da gagarumar gudummowa wajen tabbatar da manufar wannan gwamnati na bunkasa harkokin noma domin dogaro da kai da samar da abubuwan sarrafa ga masana’ntunmu da wadata kasa da abinci da samar da ayyukan yi ga dimbin al’umma.
Haka kuma ya yi wa manoman jihar Kano albishir cewa kamar yadda suka sani gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje mutum ne da yake ba harkar noma muhimmanci, domin kuwa su kansu sun isa su zama shaida yadda gwamnan ya jajirce wajen bunkasa nomada kiwo a jihar Kano ta hanyar bayar da dukkan gudummowar da ta kamata domin karfafawa manoma da makiyaya yadda za su gudanar da san’ar tasu don su samu riba. Ya ce, gwamnatin ta yi kokari wajen samar da basussuka ga manoma da kuma tallafa musu.
Faruk ce, wannan taron da suka gudanar domin taya ministan murnar samun wannan mtasayi da kuma bikin cika kwana dari na gwamnatin jihar Kano sun samu nasarar hada kan manoma da sassan jihar Kano inda suka samu wata babbar dama wajen tattaunawa a kan wadansu matsalolin da suka addabi noma akasar nan tare da kara tunawa ministan wadan nan matsaloli.
Dukkan wadanda ke da ruwa da tsaki a kan harkar noma kamar irin su kamfanonin da ke samar da inagantaccen iri da kamfanonin maganin kwari da na ciyawa da masu sayar da takin zamani da jami’an gona da manoma manya da kanan sun hadu a wajen wannan taro, wanda kuma ke nuna yadda al’ummar suka amsa wannan gayyata cike da farin ciki na nuna yadda suke da tabbacin cewa, minstan zai taimaka musu wajen ganin sun samu nasara kan hakar sana’arsu ta noma da sayar da dukkan kayayyakin da ke da dangantaka da noma.
Ya ce, saboda haka suna bugar kirji tare da yin alfaharin cewa, ministan gona zai fitar da kasar nan daga cikin matsalolin da tad ade a ciki ta fuskar bunkasa noma. Ya ce lokacin da yake shugaban hadaddiyar kungiyar manoma (AFAN) ya bayar da gagarumar gudummowa ga manoma wanda har yanzu ana ci gaba da amfana da abubuwan da ya yi, sannan kuma ya zama abin koyi ga na baya.
Baya ga wannan a wajen taron taya murnar an tattauna kan yadda za kara bunkasa harkokin noma musamman ta hanyar amfani da fasahar zamani da ilimantar da manoma kan sabbin dabarun nomad a kuma hanyoyin da za su bi wajen cin moriyar tallafin da gwamnati ke bayarwa da kuma shirye-shirye na musamman wadanda gwamnati ke gabatarwa wadanda za su taimaka wa manoman wajen habaka noma.
Saboda haka sai shugabn ya yi amfani da wannan dama ya yi kira ga manoma cewa, su tabbatar da cewa, sun yi amfani da wannan dama wajen samun ci gaba a kan sana’arsu ta noma.
Haka kuma, ya kara tabbatarwa da ministan tare da gwamnan jihar Kano cewa, za sub a su cikakken goyon baya wajen ganin sun samu nasarar aiwatar da dukkan shirin da za su gabatar wanda zai taimaki manoman wannan jiha da ma kasa baki daya.
Ya ce, domin sun fahimci irin gatan da wannan gwamnati ke kokarin yi musu na tallafa musu wajen bunkasa sana’ar tasu, saboda suma a shirye suke su ci gaba da ba gwamnatin goyon baya wajen ganin ta kai samun nasara.