Yusuf Shuaibu" />

Zabe: PDP Ta Nemi Magoya Bayanta Su Kwantar Da Hankali

Jam’iyyar PDP ta bukaci magoya bayanta su kwantar da hankalinsu a kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa wanda ya gudana ranar Asabar. Buhari ya sake lashe zabe ne da kuri’u 15,191,847, inda ya lashe Jihohi 19, tare da doke sauran ‘yan takara guda 72 ciki har da Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978, tare da samun nasara a Jihohi 17 ciki har da Abuja, inda shi ne ya zo na biyu.
Wakilin jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan sufuri Osita Chidoka, ya yi magana bayan sanar da sakamakon zaben na karshe, ya nemi magoya bayan jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, domin ita jam’iyyar PDP tana bin dokar tsarin mulkin Nijeriya tare da ban tafarkin dimokaradiyya. “Jam’iyyar PDP, jam’iyya ce wacce take bin doka da oda, muna bin doka tare da garmama dokokin Nijeriya da martaba dimokaradiyya. Amma muna da sako wanda muke son mu isar ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyamu, muna so su kwantar da hankalinsu, za mu dauki duk wani matakin ta ya dace, hanya ta farko da za mu dauki mataki shi ne, mu kai kara zuwa kotu,” in ji Chidoka.
Tun da farko dai, ya bukaci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, kar ya bayyana Buhari a matsayin wanda ya sake lashe zaben shugaban kasar. Ya bayyana cewe, mazu zabe miliyan 5.1 ba su yi zabe ba sakamakon soke zabe a wasu wurare da rashin yi wa wasu rijista a wurare da dama. Ya kara da cewa, ta ya ya za a ce Buhari ya samu kuri’u miliyan 3.9 a saman Atiku.

Exit mobile version