Connect with us

LABARAI

Zaben 2019 Ba Zai Shafi Jarabawar UTME Ba –JAMB

Published

on

Magatakardan hukumar shirya Jarabawar shiga manyan makarantu na kasar nan, Farfesa Ishak Oloyede ya ce, babban zaben kasar nan na 2019 ko kusa ba zai shafi jarabawar da hukumar za ta shirya ba na shekarar 2019/2020.
Magatakardan ya yi wannan tsokacin ne sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan da gama jawabin da ya yi a wajen taron shekara-shekara na, Sobo Sowemimo, na Klub din Abeokuta, a can Abeokuta din.
Oloyede ya ce, tun da dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayar da bayanin ranakun da za a yi zabukan, to hukumar ta su tana bukatar ta gyara na ta ranakun ne kadai.
Ya kuma koka kan yadda wasu da ba su cancanci rubuta jarabawar ba, suke neman a ba su daman rubutawa, wanda a cewar sa hakan yana kara wa hukumar na su nauyi ne kawai.
Ya ce, hukumar ta JAMB za ta dauki tsauraran matakai na ganin ta kore duk wadanda ba su cancanci rubuta jarabawar ta 2019/2020 ba, daga neman yin hakan.
Magatakardan kuma ya ce, hukumar za ta fara shirin gudanar da jarabawar na shekarar 2019/2020, ne daga watan Oktoba, ya kuma yi alkawarin tsarin tafiyar da jarabawar na wannan shekarar zai fi na bara kyau.
“A yanzun haka, tun a watan jiya muka fara shirin jarabawar ta 2019/2020. Muna da tabbacin daga nan zuwa karshen watan Oktoba, za mu fara daukan na wannan shekarar ta 2019/2020.
“Ina tabbatar maku muna duba duk ‘yan kurakuran da muka yi a bara. Muna kuma gyara su domin tabbatar da ba wanda zai wahalar da wasu ba tare da laifin su ba.
Oloyede, bai bayyana yawan wadanda ake sa ran za su yi rajistan daukan jarabawar ba ta 2019, amma ya ce za a dauki matakan ganin an rage yawan masu daukan jarabawar daidai gwargwado.
“Yana da wahala a ce ga yawan wadanda za su dauki jarabawar a yanzun. Amma muna sa ran rage yawan su matuka, saboda da yawan masu karban fom din sam ba su ma shirya wa jarabawar ba.
“Wasu daga cikin daliban SS1 wadanda suke ta himman biyan Naira 5,000 haka siddan a cikin asusunmu. Muna ta dai yin tsare-tsaren tabbatar da cewa duk wadanda suka yi rajistan sun cancanci daukan jarabawar ne.
“Mu ba kudin ne damuwan mu ba. Sha’awarmu a samu daliban da suka cancanta ne,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: