Sabo Ahmad" />

Zaben 2019: Danbwambo Ya Nemi Goyon Bayan Wakilan PDP Daga Yankin Arewa Maso Yamma

A matsayinsa na daya daga cikin wadanda suke neman jam’iyyar PDP ta ba su damar tsaya wa takarar shugabn basa a zabe mai zuwa na shekara ta 2019 gwamnan jihar Gombe Ibrahim Danbwambo ya nemi goyon bayan wakilan da za su zabe daga shiyyar Arewa maso Yamma kan bubatarsa ta zama dantakar shugaban basa a inuwar jam’iyyar PDP lokacin day a kawo ziyara Kaduna a ranar litinin din da ta gabata.

Danbwambon ya bayyana hakan ne lokacin da yake zaman tattauna wa da wakilan a cikin makon da ya gabata, inda ya robi su da su ba shi goyon baya matubar ya samu tikitin jam’iyyar na takarar shugaban basa.

Da yake bayyana kansa a matsayin wanda ya cancanta ya zama shugaban basa domin fitar da basar nan da al’ummar basar daga cikin halin bangin da suka fada, haka kuma ya bayyana cewa ya fara miba wannan bubata ta sa ce da wakilan na wannan shiyya, domin shiyya ce da take da wahalar cin zaben shugaban basa.

“Akwai masu zabe sama da nutum miliyan goma sha takwas a wannan shiyyar wadanda dukkan wani mai neman takara ba zai taba yin sako-sako da ita ba, wajen neman buri’arsu ba.

“Haka kuma shiyyar na da wakilai masu yawa a jam’iyyar PDP da za su yi zaben fid da gwani,” Ya ce, duk wanda ya samu rinjaye a wannan shiyyar to ne zai samu nasarar zama dantakara a 2019.

Saboda haka sai gwamnan ya robe su da su zabe shi, wanda kuma ya tabbatar musu da cewa, matubar jam’iyyar PDP tab a shi tikitin tsayawa takarar shugaban basa, yana da jama’ar da za su zabe shi a fadin basar nan.

Hak kuma ya kira ga wakilan su ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar katin buri’a, domin kuwa das hi ne kowa zai zabi abin da yake so ya zaba.

Haka kuma Danbwambon ya bara nuna muhimmancin sanar da jama’ar ranar da Hukumar zabe ta ajiye a matsayin ranar barshe ta karbar buri’a.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa, mataimaki shugaban jam’iyyar PDP na wannan shiiyar Ibrahim Kazaure, da babban sakataren jam’iyyar na basa Umar Ibrahim Tsauri,da shugaban jam’iyyar da sakatare na jihar Kaduna da Kano da Jigawa da Zamfara da Kebbi da Sakkwatoda Katsina duk sun halarci wannan taron.

Bayan gwamna Danbwambo akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi da tsohon mataimakin shugaban basa Atiku Abubakar da shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal. Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar  Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso da Ibrahim Shekarau, da tshon gwamnan jihar Sakkwato Attahiu Bafarawa, wadanda dukkaninsu sun nuna bubatarsu ta tsaya wa takarar shugaban basa, a inuwar jam’iyyar ta PDP.

Exit mobile version