Akalla gwamnoni shida masu barin gado ne a fadin kasar nan suka gaza kai bantensu bayan tsayawa takarar kujerar Sanata a mazabunsu.
Gwanonin wadanda suka yi wa’adin shekara takwas a kan kujerunsu, sun sha kasa ne a zabukan Sanatan da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabirairu 2023.
- Da Dumi-Dumi: PDP, LP Da ADC Dun Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sabon Zabe
- Peter Obi Ya Lashe Birnin Tarayya
Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, an danganta majalisar wakilai da kuma ta dattijai a matsayin wata mafakar tsofaffin gwamnoni.
Kimanin tsofaffin gwamnoni 20 aka zaba zuwa ga majalisa ta tara a 2019.
Tsofaffin gwanonin da a yanzu ke majalisar dattawa su ne, Rochas Okorocha daga Jihar Imo, Ibikunle Amosun daga Jihar Ogun, Abdulaziz Yari daga Jihar Zamfara Kabiru Gaya daga Jihar Kano, Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa, Chimaroke Nnamani daga Jihar Enugu, Kalu daga Jihar Abia, Gabriel Suswam daga Jihar Binuwe da kuma Ibrahim Shekarau daga Jihar Kano da sauransu.
Wadanda a bana suka shiga zaben sun hada da, gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi, gwamnan Jihar Neja Abubakar Bello da kuma gwamnan Abia Okezie Ikpeazu wadanda suka lashe zaben na ranar asabar.
Sai dai, Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya fadi yayin da ba a bayyana na gwaman Sakkwato Aminu Tambuwal ba.
Tsofaffin gwanonin da suka lashe zaben Sanata su ne, Adams Oshiomhole daga Jihar Edo sai kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio.
Ga jerin sunayen gwamonin masu barin gado da suka gaza lashe zaben bayan sun kammala wa’adin mulkinsu a watan Mayu 29, 2023.
Dan takarar Sanata na APC Titus Zam ya kayar da Samuel Ortom gwaman Jihar Binuwe a zaben Sanata na mazabar Binuwe ta Arewa Maso Gabas, inda Zam ya samu kuri’u 143,151, Ortum gwannan PDP na G-5, ya samu kuri’u 106,882, sai LP ta samu kuri’u 51,950.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya gaza lashe zaben Sanata na mazabar Enugu ta Gabas.
Dan takarar Sanata a LP Okechukwu Ezea ne INEC ta sanar ya lashe zaben, inda ya samu kuri’u 104,948, Ugwuanyi kuma ya samu kuri’u 46,948.
Akwai kuma gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku wanda ya sha kasa a zaben mazabar Taraba ta Kudu, inda dan takara David Jimkuta, daga APC ya kayar da shi bayan ya samu kuri’u 85,415 Ishaku kuma ya samu kuri’u 45,708.
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong kuma darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, dan takarar Sanata a PDP Bali Ninkap Napoleon ya kayar da shi bayan ya samu kuri’u 148,844 inda Lalong ya samu kuri’u 91,674.
Gwannan Jihar Koros Ribas Ben Ayade ya sha kasa a hannun Jarigbe Agom-Jarigbe dan takarar Sanata a jam’iyyar PDP, wanda dama can shi ne yake a kan kujerar, inda Agom ya samu kuri’u 76,145 sai kuma Ayade ya samu kuri’u 56,595.
Ayade kafin a zabe shi gwamna, ya kasance zababben Sanata ne daga
2011 zuwa 2015, inda a zaben 2023, ya so ya sake komawa majalisar dattawa
don ya wakilci mazabar Koros Ribas ta Arewa.