Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da kada ya ba kansa nasara a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na shekarar 2023, yana mai cewa gwamnonin Arewa da yake sa ran za su ba ba shi kuri’u sun gaza sosai.
Kwamitin ya kuma bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya ja kunnen Tinubu kan yin ikirarin nasara a zaben na 2023.
- INEC Ta Dage Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Tarayya Zuwa Yau Lahadi A Yenagoa
- Atiku Ya Lashe Rumfar Zaben Mataimakin Peter Obi, Datti Baba-Ahmed
Kwamitin kamfen din ya bayyana hakan lokacin da yake mayar da martani ga wata kafar yada labarai da ta buga wanda PDP ta ce mallakin Tinubu ne.
Kafofin yada labaran sun yi ikirarin cewa Tinubu ne ke kan gaba a shiyyar Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya na kasa.
Sai dai Daraktan Sadarwar da Dabaru na
Kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, Cif Dele Momodu, wanda ya sanya hannu a wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce Tinubu ne kadai dan takara daya tilo da jam’iyyun adawa suka lalata yankinsa na Kudu maso Yamma a jihohin Legas, Ogun, Ondo, Oyo, Osun da Ekiti.
Ya ce, “Dazun nan hankalinmu ya karkata ga labarin da jaridar ta buga mai hatsarin gaske da ke bayar da nasara ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu. Jaridar da aka ce mallakin Tinubu ce.
“A jiya ne muka ga yadda ’yan barandar APC da mutanensu suka mamaye titunan Legas suna kona akwatunan zabe da takardu da kuma nuna rashin da’a.
Duk da yunƙuri na satar nasara, APC ta yi asarar mafi muni a mafi yawan wuraren zaɓe a Legas. Haka ya faru a Kano.
A safiyar yau mun wayi gari mun karanta labarin karya da karyar da jaridar Tinubu suka buga.
“Tinubu ya dan takara ne daya tilo da jam’iyyun adawa suka lalata masa Kudu maso Yamma a Legas, Ogun, Ondo, Oyo, Osun da Ekiti. Yawancin Gwamnonin Arewa da ya sa ran za su taimaka masa wajen samun kuri’u a yankunan Arewa sun kasa kai wa ga kuri’un da ake bukata. Ya gaza a Kudu maso Gabas da Kudu Kudu.
“Dan takara daya tilo a kasa shi ne dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a matsayinsa na dan kasa mai kishin kasa, ba zai taba yin gaggawar shiga kafafen yada labarai don neman nasara.” cewarsa.