Ibrahim Muhammad" />

Zaben Doguwa Da Tudun Wada: ‘A Matsayina Na Dan Takarar PDP An Hana Ni Yin Zabe A Akwatin Mazabata’

Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar PDP a zaben raba gardama da aka gudanar na kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa, Kwamandan Sojan sama mai ritaya, Salisu Abdullahi Yusha’u ya bayyana sam ba’a bar shi yama fito daga gidansa ba shida iyalinsa balle har ya kada kuri’arsa a sakamakon dinbin yandaba da aka jibge dauke da makamai daf da gidan da yake a karamar hukumarsa ta Tudun wada.

Yusha’u ya ce duk kuwa da dinbin jami’an tsaro da aka kawo amma hakan bai hana jam’iyya masu mulki su shigo da dinbin yan daba yankin ba, suka tashi hankalin kowa dan haka ma mutane musamman masoya jam’iyyar ta PDP suka janye jikinsu dan gudun kar a zubar da jini domin kuwa yan PDP Kwankwasiyya masu kaunar zaman lafiya ne.

Ya kara da cewa ganin an kawo jami’an tsaro sun zaci zasu aikinsu dan baiwa kowa dama yayi zabe amma sai gashi a gabansu aka rika gudanarda abubuwa da suka saba ka’idar zabe.

Kwamandan Sojan sama mai ritaya ya ce a lokacin zaben wasu daga mutanensu a wuraren akwatunan zabuka daban-daban sun yita kiransa a waya suna cewa an hanasu zuwa suyi zabe a akwatunansu na zabe nace musu nima ba’a barni na sami damar fitowa dafa gida bama bare inje inyi zaben saboda yandaba da aka jibge.

Ya ce wannan abu abin takaicine an hana mutane masu yanci su zabi muradinsu anyi musu karfa-karfa da sunan anyi zabe.

Kwamandan sojan saman mai ritaya ya mika godiyarsa ga al’ummar Tudun wada da Doguwa bisa yanda suka nuna sanin yakamata suka kaucewa duk wani abu dazai musabbabin zubda jinin al’ummar yankin ta janye jikinsu daga wuraren zaben ya ce wannan abu da akayi da sannu zasuga sakayyar ubangiji bisa wannan danniya da akayi musu.

Exit mobile version