Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a cikin harkokin zabe, kamar su jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da kuma manema labarai kan sabon yunkurin shirye-shiryen zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo.
Wannan ita ce ganawa irinta ta farko tun bayan kammala zaben cike gurbi da ya gudana a watan Fabrairun 2024, a jihohi 26 da ke fadin kasar nan.
Babban makasudin taron shi ne, yadda za a samu nasarar gudanar da sahihin zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo. Zaben gwamnan Jihar Edo zai gudana ne a ranar 21 ga Satumbar 2024, yayin da za a yi zaben gwamnan Jihar Ondo a ranar Asabar, 16 ga Nuwambar 2024.
Tuni dai jam’iyyu suka gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnan Jihar Edo. A cewar jadawalin zaben, jam’iyyu suna da kwanaki 21 ne kacal wajen mika bayanan ‘yan takararsu ga hukumar zabe.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci ganawar ya bayyana cewa hukumarsa ta horar da jami’an jam’iyyu na yankuna ta yadda za a taimaka wa dukkan jam’iyyun siyasan. Ya kara da cewa sun bude adireshin amsar bayanan ne tun a ranar 4 ga Maris, 2024, sannan kuma suka rufe da misalin karfe 6 na yamma na ranar Asabar, 24 ga Maris ta 2024.
A cewarsa, bayan makonni biyu aka sake budewa saboda ba dukkan jam’iyyu suka saka bayyana ‘yan takaransu ba.
Hukumar INEC ta yi kira ga jam’iyyun siyasa su ci gaba da bin jaddawalin ayyukan zaben domin kaucewa rudadi.
Za dai a fara gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnan Jihar Ondo a ranar 6 ga Afrilun 2024, wanda za a kammala a ranar 27 ga Afrilun 2024. A ciki jam’iyyun siyasa 19, 16 ne kadai suka nuna sha’awarsu ta shiga zaben.
Da yake jawabi, shugaban gamayyar jam’iyyu, Yusuf Dantalle ya bayyana cewa babu uzuri matukar an gaza gudanar da zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo yadda ya kamata.
Jihohin Edo da Ondo dai kowannensu yana da kananan hukumomin 18. Yayin da Jihar Edo take da masu rajistar zabe guda 2,501,081, cibiyoyin zabe 192 da kuma rumfunan zabe 4,519, inda Jihar Ondo take da yawan masu rajistar zabe guda 1,991,344, cibiyoyin zabe 203 da kuma rumfunan zabe 3,933.