Manyan jam’iyyun siyasa da suka shiga cikin zaben neman kujerar gwamnan Jihar Edo da za a yi a ranar 21 ga Satumba, sun kammala zaben fitar da gwani mai cike da rudadi kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, (INEC) ta ayyana cikin jaddawalin ayyukan zaben.
A daidai lokacin da kowacce jam’iyya cikin manyan jam’iyyun siyasa kamar APC, PDP da LP suke fama da rikice-rikicen cikin gida tun kafin zaben fitar da gwani, masana sun yi hasashen shugabannin manyan jam’iyyun za su samu nasarar sulhunta rikice-rikicen, amma kuma lamarin ya ci tura, yayin da aka samu zaben fitar da gwani kashi-kashi a cikin jam’iyyun wanda ya raba kan ‘yan takara har aka samu ‘yan takara biyu zuwa uku a jam’iyya guda daya.
- Kwamitin Majalisa Zai Kammala Garanbawul Na Kundin Tsarin Mulki Cikin Wata 24
- Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi
Kafin zaben, INEC ta gargadi jam’iyyun guda 16 cikin 18 da suka yi rajistar shiga zaben kan su yi kokarin gudanar da zaben tifar da gwani kamar yadda hukumar ta ayyana tare da sanar da rana da lokacin zaben fid da gwanin domin ya zama ya dace da abin da doka ta tanada.
Babban kwamishinan yada labarai da ilmantar da masu zabe na INEC, Sam Olumekun, ya bukaci jam’iyyun siyasan su kula da dage-dagen zaben fitar da gwani da sauye-sauyen wuraren zaben ba tare da ka’ida ba da kuma uwa uba kan canza ‘yan takarar da suka lashe zaben fitar da gwanin.
Ya kuma yi kira da jam’iyyun su guji karya ka’idojin zaben fitar da gwani wanda hakan zai kai ga karya dokokin zabe kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
“Akwai wasu abubuwa da ke haddasa matsaloli a wurin zaben fitar da gwani. Doke ne jam’iyyun su tura wa hukumar INEC rana da lokacin da za su yi zaben fitar da gwani a shafinmu da kuma sauran kafafen yada labaranmu domin sanar da mutane,” in ji Olumekun.
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa idan har da jam’iyyun sun ji gargadin hukumar zabe da sun samu nasarar magance wadannan matsalolin da suka ta so lokacin zaben fitar da gwanin.
Mafi yawancin ‘yan takarar sun ki amincewa da rashin nasara da kuma yadda aka yi zaben fitar da gwanin a dukkan jam’iyyun, wanda hakan babban barazana ce ga harkokin zabe.
A bangaren APC, a sabon zaben fitar da gwani da ta yi a ranar Alhamis, an tabbatar da cewa Sanata Monday Okpebholo ba shi ne asalin dan takarar da tsoohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yake so ba, wanda ya kasance shi ne jigon APC a jihar.
Ana fargabar cewa idan har ba a gudanar da zaben fitar da gwani yadda ya dace a jam’iyyar APC ba, dan takarar Oshiomhole, Dennis Idabosa da wasu sauran ‘yan takarar guda 10 sun fusata, wadanda za su iya yakar APC a zaben. Idan dai za a iya tunawa, APC tana neman yadda za ta sake kwace shugabancin jihar daga wurin PDP bayan ta samu irin wannan matsala a 2020, wanda ya sa ita PDP ta kwace mulki a jihar.
Idan za a iya tunawa dai APC ta fara gudanar da zaben fitar da gwani ne a ranar 17 ga Fabrairu, amma kuma zaben ya zo da rudani da aka gudanar da wurare daban-daban a garin Benin, babban birnin Jihar Edo, wanda aka samu ‘yan takara guda uku suke ikirarin samun nasara.
Dan majalisar wakilai, Dennis Idahosa, wanda ya kasance dan takarar da ke samun goyon bayan Oshiomhole, kwamitin gwamna Hope Uzodimm ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na APC a otel din Protea da ke cikin garin Benin.
Shi ma Sanator Monday Okpebholo, babban jami’in zaben, Dakta Stanley Ugboaja ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a gidan Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Kazalika, jami’an da suka kula da zaben a kananan hukumomi, sun ayyana Anamero Sunday Dekeri a matsayin wanda ya yi nasara. An dai samu wasan kwaikoyo wanda kowani daya daga cikin ‘yan takaran yake ikirarin nasara, har sai da uwar jam’iyyar APC ta sake sabon zaben fitar da gwani a ranar Alhamis da ya gabata.
A yanzu dai, ta tabbata cewa Sanata Monday Okpebholo shi ne ya yi nasarar samun tikitin zaben fitar da gwani karkashin jagorancin gwamnan Jihar Kuros Ribas, Bassey Otu, wanda ya canji gwamna Uzodimma bayan da masu ruwa da tsaki suka gudanar da zanga-zanga. Sai dai kuma samun narasarar Okpebholo a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Edo karkashin tutar jam’iyyar APC zai samu kalubale mai yawan gaske, domin wasu daga cikin ‘yan takarar ba za su goyi bayansa ba.
Bangaren PDP
Zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP ya rabu kashi-kashi, yayin da mataimakin gwamnan, Philip Shaibu da sauran ‘yan takara suke ikirarin samun nasara.
Akwai ‘yan takara guda 10 a PDP da suka hada da Shaibu, Omoregie Ogbeide-Ihama, Anselm Ojezua, Felid Akhabue, Martin Uhomoibhi, Hafia Hadizat Umoru, Omosede Igbinedion, Earl Osaro Onaiwu, Arthur Esene da kuma Asue Ihgodalo.
Jam’iyyar PDP tana fatan ci gaba da rike kambunta na mulkin jihar, rikici ya farke ne lokacin taron kananan hukumomi na kwamitin jam’iyyar na mutum uku karkashin jagorancin gwamnan Jihar Inugu, Peter Mba. Bayan taron, ‘yan takara tara sun yi zargin rashin adalci a taron.
Duk da yake gwamna Obaseki bai fito fili ya nuna goyon bayansa karara ga Ighodalo ba, amma alamu sun nuna yana goyon bayansa.
A ranar 22 ga Fabrairu, jam’iyyar ta rabu gida biyu wanda kowani bangare ya gudanar da zaben fitar da gwani. Daya bangaren, zaben ya gudana ne a filin wasa na Ogbemudia da ke Benin, yayin da shi kuma daya bangaren ya gudanar da nashi a masaukin mataimakin gwamnan da ke Benin.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal shi ne shugaban kwamitin kuma babban jami’i mai kula da zabe, ya ayyana Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP da ya gudana a filin wasa na Ogbemudia, wanda ya samu kuri’u 577, a bangaren daya kuma, Shaibu ya lashe zaben fitar da gwani da babban jami’an kula da zaben, Bartholomew Moses ya sanar a masaukin mataimakin gwamna da kuri’u 300.
Sai dai mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wani dan takara sai dai Asue Ighodalo shi kadai.
Jam’iyyar LP
Kokarin fitar da dan takara a jam’iyyar LP ba ta sauya zani ba, kamar yadda lamarin yake a APC da PDP da ke cike da rikice-rikice.
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa shugaban jam’iyyar na kasa, Julius Abure da shugaban jam’iyyar na jihar, Kelly Ogbalu da kuma sanatan da ke wakitar Edo ta kudu, Neda Imasuen duk suna da mabambantan ‘yan takara da suke marawa baya.
‘Yan takarar sun hada da Olumide Akapta, Kenneth Imansuangbon, Farfesa Sunday Eromosele da kuma Sergius Ogun. Zaben fitar da gwanin a jam’iyyar ya kasu zuwa gida biyu, wadanda suka gudana a otel din Uyi da cibiyar Bishop Kelly.
Imasuagbon da magoya bayansa sun yi zaben nasu ne a otel din Uyi, yayin da kwamitin da uwar jam’iyyar ta kafa suka gudanar da zaben a cibiyar Bishop Kelly.
Daga baya dai Imasuagbon ya ziyarci cibiyar Bishop Kelly, inda aka bayyana Akpata a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 316.
A halin yanzu dai, bangaren shugabancin jam’iyyar karkashin Lamidi Apapa sun mika wa hukumar INEC sunan, Anderson Uwadiae Asemota da Monday Ojore Mawah, a matsayin dan takarar gwamna da mataimakinsa na zaben gwamnan Jihar Edo da zai gudana a ranar 21 ga Satumba.
Amma kuma wani bangare na shugabancin jam’iyyar ya ce INEC kar ta amince da sunayen da aka tura matasa a matsayin wadanda suka lashe zaben fitar da gwani na LP, domin ba su cika ka’ida ba.