Bello Hamza">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Zaben Kananan Hukumomi: APC Ta Kama Hanyar Lashe Dukkan Kujeru A Kano

by Bello Hamza
January 17, 2021
in LABARAI
2 min read
APC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • An Samu Karancin Masu Zabe
  • An Kafa Kotun Sauraren Korafin Bayan Zabe

Daga dukkan alamu jam’iyya mai mulki na APC ta kamo hanyar lashe dukkan kujerun kananan hukumomin jihar Kano 44 da kuma dukkan kasilolinsu gaba daya, rahotannin daga runfunan zaben da aka gudanar jiya Asabar 16 ga watan Janairu yana nuna cewa, duk da an samu karancin masu jefa kuri’a, jami’iyyar APC ce ke kan gaba a kusan dukkan runfunan zaben da wakilimu ya zagaya haka kuma rahoton yake fitowa daga sauran kananan hukumokin jihar, bayani ya kuma nuna cewa, an gudanar da zabbukan cikin kwanciyar hankali ba tare wani gaggarumin rikici ba.

Wuraren da wakilinmu ya ziyarta sun hada da Chedi, Zage, Zango, Gandu, Sharada, Wailawa, Dorayi, Kabuga, Rijiyar Zaki a karamar hukumar Kano Municipal, Gwale, da kuma karamar hukumar Ungogo.

An dai fara zaben ne a daidai karfe 10:30 kamar yadda aka shirya are da kasancewa, jami’an tsaron.

Wasu da wakilinmu ya tattauana da su sun nuna jin dadin su akan yadda suka ga ake gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba sun kuma yada wa hukumar zaben akan yadda ta horas da ma’aikatan, don kuwa suna gudamar da ayyukan su ne ciki ne kwarewa.

Hukumar ta kuma samar da ma’aikata 48,000 da za su yi aiki a runfunar zabe 11,500.

Haka kuma babban jojiin jihar Kano, Maishari’a Nura Sagir, ya kafa kotuna biyu da za su karbi kofa-korafe da za su fito daga zaben da aka gudanar.

Bayanin haka na kunshe ne a takarar sanarwa da jami’in watsa labarai nan ma’aikatar shari’ar, Mr Baba Jibo-Ibrahim, ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Kano ranar Asabar.

“Kamar yadda ya ke a sashina 36(1) na dokokn zabe na jihar Kano na shekarar 2002, kotu nan za su saurari tare da yanke hukunci kan zabukkan da ke gudanarwa a yau Asabar,” inji shi. Ya kuma kara da cewa, sauran bayanai akan kotunan na zuwa a nan gaba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Kasa Ya Nada Buba Marwa Shugaban NDLEA

Next Post

An Nada Farfesa Maimuna Matsayin Shugabar Jami’ar FUGA 

RelatedPosts

An Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona

An Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona

by Bello Hamza
1 hour ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim An yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da...

Mukabalar

Kotu Ta Dakatar Da Yin Mukabalar Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano.

by Bello Hamza
7 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Wata kotu a Jihar Kano ta...

Ma'adanai

Masu Hakar Ma’adinai Ba Su Da Alaka a‘Yan Ta’adda -Shugaba

by Bello Hamza
7 hours ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Shugaban kungiyar masu hakar ma'adinai ta  Nijeriya...

Next Post
An Nada Farfesa Maimuna Matsayin Shugabar Jami’ar FUGA 

An Nada Farfesa Maimuna Matsayin Shugabar Jami'ar FUGA 

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version