Daga Lawal Umar Tilde, Jos
Fargabar da Jam’iyyar APC ke yi a jihar Filato na ganin ba za ta yi nasara ba a zabubbuka masu zuwa a jihar ya sa ta kasa gudanar da zaben Kananan Hukumomi. Wannan furucin ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar ‘Transform Nigeria Group {TNG}’ tya matasa, karkashin jam’iyyar PDP, rashen jihar Filato, Kwamared Idris Zahiru Umar a lokacin da yake tattaunawa da Wakilinmu a kwanakin ba ya.
Ya ce jihar Filato jiha ce ta jam’iyyar PDP, tun dawowar gwamnatin Dimokurdiyya har yanzun nan tana da karfi a kowane lungu na jihar.
Kwamared Umar, wanda ya ce a zaben 2015, jam’iyyarsu ta PDP ta lashe kujerun Senatoci Uku da na ‘yan Majalisar wakilai na Tarayya Shida, da ‘yan Majalisar Dokoki na jihar guda goma sha uku. Ya ce hangen Dala ne kawai mutanen jihar suka yi wa jam’iyyar APC, ya sa suka zabeta, amma a shekaru biyu din nan da Gwamnan ya yi a ofis ya nuna masu a fili sun yi zaben tumun dare.
Shugaban ya ce, rikicin da ya addabi uwar jam’iyyar na kasa babban darasi ne da ya karantar da dukkan ‘yan jam’iyyar, wanda hatta tsohon Shugaban, kasa GoodLuck Jonathan, a wani taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ya amince cewa an yi kuskure, kuma ya ce a zabubbuka masu zuwa na 2019, dan takarar shugaban na jam’iyyar zai fito ne daga Arewa, wanda ya ce hakan zai baiwa jam’iyyar dama ta kafa gwamnati .
Daga nan sai Zahiru Umar ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga ’yan jam’iyyar don zabar shugabanni nagari da za su jagoranci al’ummar kasar nan cikin nasara. Ya ce mutane irin su Barista Tanimu Turaki ne suka cancanta a zaba su shugabanci kasa a 2019. Ya ce domin ya yi an gani a lokacin da yake rike da mukamin Minista.