Jam’iyyun adawa a fadin kasar nan na zargin jam’iyyun da ke mulki a jihohi da gwamnoninsu da tozarta dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi ta hanyar rantsar da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ba tare da gudanar da sahihin zabe ba.
Sun bayyana cewa mafi akasarin zabukan shugabannin kananan hukumomi da gwamnoni suka yi sun barnatar da dukiyar al’umma ne kawai da sunan zabe.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Bunƙasa Tattalin Arziƙi: Shettima Ya Tafi Kasar Sweden Ziyarar Aiki Ta Kwana Biyu
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar a fadin tarayyar kasar nan ya nuna cewa zaben kananan hukumomi ya kasance ana goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyu masu mulki da makusantan gwamnoni, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta jihohi (SIEC) ta bayyana a matsayin wadanda suka lashe zaben da ba a yi ba bisa ka’ida ba.
A cewarsu, tun daga tsare-tsare har zuwa matakin zartarwa, SIECs sun nuna kyama ga jam’iyyun adawa.
A zaben kananan hukumomi na 2024 a Jihar Oyo, kimanin mutane miliyan uku ne suka cancanci kada kuri’a, sama da ‘yan takara 4,900 da jam’iyyun siyasa 18 ne suka shiga zaben.
Zaben ya gudana ne a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, 2024 a fadin kananan hukumomi 33 da kuma gundumomi 351 na jihar.
Bayan kammala zaben ne hukumar zaben jihar OYSIEC ta sanar da sakamakon zaben mai cike da rudani, yayin da jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe dukkan zaben.
Sai dai bayan sanar da sakamakon zaben a hukumance daga dukkanin kananan hukumomi 33 da aka gudanar da zabe, an samu korafe-korafe daga wasu kananan hukumomi game da sabanin da aka samu a lokacin gudanar da zaben, wanda ya hada da jinkirin jami’ai da kayan aiki da kuma rashin samar da kayayyakin da suka dace.
Daya daga cikin jam’iyyun siyasar da suka shiga zaben, AAC ta nuna rashin jin dadinta da yadda aka gudanar da zaben tare da yin kira da a soke zaben.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Fami Adeyeye, ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Oyo ba ta gudanar da sahihin zabe ba.
Haka zalika, babbar jam’iyyar adawa ta APC ta bayyana zaben a matsayin shirme.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Wasiu Olawale Sadare, ya ce idan aka ci gaba a haka, to irin wannan zabe zai iya haifar da rudani a jihar.
A Jihar Kebbi, an gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a ranar Asabar, 31 ga watan Agusta, a dukkan kananan hukumomin jihar 21. Jam’iyyun siyasa 18 daga cikin 19 ne suka shiga zaben, in ban da jam’iyyar PDP da ta fice daga zaben makonni biyu kafin ranar zaben.
A karshe dai, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta sanar da cewa jam’iyyar APC ce ta lashe dukkan zaben shugabanni kananan hukumomi 21 da kansiloli 223 na jihar.
Sai dai sakataren jam’iyyar PDP na jihar, Abubakar Bawa Kalgo ya ce jam’iyyarsu ta fice daga zaben ne saboda magudi da kuma rashin amincewar hukumar zaben jihar.
‘Yan adawar dai sun koka tare da zargin jam’iyya mai mulki da tafka magudi a zaben shugabannin kananan hukumomi, suna masu cewa a zaben gaskiya da adalci, ba zai yiwu jam’iyyar siyasa daya tilo ta lashe dukkan kujerun ba.
A Jihar Sakkwato, an gudanar da zaben kananan hukumomi 23 a ranar 21 ga watan Satumba, 2024, inda jam’iyyar APC mai mulki ta samu gagarumin rinjaye.
Ko da yake sauran jam’iyyun siyasa 15 ne suka shigar da ‘yan takara a zaben a cewar hukumar zaben jihar, sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta shiga zaben ba.
Zaben kananan hukumomin Jihar Gombe da aka gudanar a ranar 27 ga watan Afrilu, jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugaban kananan hukumomi 11 da na kansiloli 114.
Gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a karo na biyu a cikin shekaru biyar, amma jam’iyyun adawa sun koka, inda suka ce an tafka magudi da rashin gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe da dama.
An bayyana ‘yan takarar jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka lashe dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi 16 da kansiloli 193 na jihar.
Sai dai dan takarar shugaban karamar hukumar Illorin ta yamma daga jam’iyyar adawa ta PDP, Musbau Esinrogunjo ya yi watsi da sakamakon zaben.
An gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Borno a watan Janairun 2024, inda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin da kansiloli a kananan hukumomi 27. Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Borno, Alhaji Zanna Gaddama, ya yi tir da zaben a matsayin abin ban mamaki, inda ya zargi jam’iyya mai mulki da kirkirar sakamakon zabe na bogi.
A Jihar Jigawa, zaben kananan hukumomin da aka gudanar a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024, ya kunshi jam’iyyun siyasa 12, inda jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 27 da kansiloli 281 daga cikin kujeru 287 na kansiloli. Jam’iyyun APGA da AP sun lashe kujerun kansila daya da hudu, bi da bi. Shugaban jam’iyyar APC, Hon. Aminu Sani Gumel ya bayyana jin dadinsa da yadda zaben ya gudana, inda ya bayyana cewa an yi zaben cikin lumana da adalci.