A zabubbukan kanannan hukumomi na kwanakin baya, da aka gudanar a wasu jihohin kasar nan, gwamnonin jihohin, sun yi ta hakilon yin karfakarafa domin ganin cewa, ko ta halin kaka, sai ‘yan takararar su ne, suka lashe zabubbukan.
Misali a makonni ukun da suka gatabata, an gudanar da zabubbukan kanannan hukumomi a jhohin Anambra, Kwara, Kebbi, Ribas, Biniwe, Akwa Ibom, Filato da dai, sauransu.
Hakazalika, ma jihohin Kano da Kaduna, suna ci gaba da kai gwauro su kai mari, domin ganin sun dora ko nada ‘yan takarar jam’iyyunsu a zabubbukan shugagannin na kanannan hukumomin.
Hukumomin gudanar da zabubbukan na kananan hukumomi masu zaman kansu na jihohin da kundin tsarin mulki kasar na shekarar 1999 da aka sabunta, ya dora masu alhakin gudanar da dabubbukan bisa adalci.
Sai dai, kuma abin takaici, akasarin zabubbukan na kanannan hukumomin da aka gudanarwa, cike suke da tabka magudin da kusan ma ya wuce hankali.
Hakanan ma, wani da ya zama tamkar gari a yayin gudanar da zabubbukan na kanannan hukumomi a kasar shi ne, yadda jam’iyyar da ke rike da madabun iko a jihohin, galibi ‘yan takararta ne, suke lashe zabubbukan, kusan tun daga na shugaban karamar hukuma har zuwa na Kansiloli.
Sai dai kuma, an samu wani dan karamin sauyi a jihar Akwa Ibom, inda jam’iyyar adawa ta APC, ta lashe zaben karamar hukuma daya kacal a jihar.
An dai sha zargin gwamnonin jihohin wajen yin amfani da ‘yan korensu don yin karfa-karfar tabka magudin zabe.
Misali, a jihar Ribas, a zabubbukan kanannan hukumomi na jihar da aka yi bada dadewa ba, an zargi gwamnan jihar Siminalayi Fubara da tabka irin wannan kazamin magudin, zaben, inda jam’iyyar APP da goyawa baya a lokacin zaben, ta samu gaggarumar galaba, a kan sauran jam’iyyun adawa da suka fafata a zaben.
Jam’iyyar ta APP ta lashe zabubbukan ne, saboda goyon bayan da ta samu daga gun gwamna Fubara, ta hanyar nada masu yi masa biyayya a matsayin jami’an hukumar zaben jihar da suka gudanar da zabukan.
Bugu da kari kuma wadannan jami’an hukumar zaben, sun samu sahalewar ‘yan majalisar dokokin jihar da Fubura ke juya su kamar Waina, don su gudanar da zabubbukan tun daga Kujerar shugabannin kananan hukumimin har zuwa Kujerar Kansilpli.
A irin wadannan zabubbukan, cike suke da magudi da abin al’ajabi, domin tun kafin ma a sanar da sakamkon zabukan, aka fara taya ‘yan takarar jam’iyya mai mulki, murnar lashe zabe.
Yana da kyau a gane lamarin, duk da cewa, irin yakin da kanannan hukumomin kasar suka sha fama suna yi, na sai sun samu ‘yancin cin gashin kansu, wanda daga bisani, suka yi nasara bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukuncin ba su damar cin gashin ‘yancin kansu, amma ga dukkan alamu, har yanzu kusan yakin bai kare baa kwai sauar rina a kaba.
Idan har yanzu ba a samar da tsarin gudanar da sahihan zabubbukan a kanannan hukumomi ba, idan aka lura da yadda gwamnonin jihohin ke yin amfani da dukkan karfin ikon da suke da shi don ganin ‘yan takarar jam’iyyun su, sun samu nasara, to za a iya cewa, tamkar an kashe Maciji ne, amma ba a sare kansa ba.
Amma domin a kawo karshen irin wannan kwamacalar a zabubbukan kanannan hukumomi, wannan jaridar, na son kara jaddada kiranta na a soke hukumomin gudanar da zabe masu zaman kansu na jihohi.
Maimakon haka ma sai a bar hukumomin zaben su rinka gudanar da zabubbuka, kamata ya yi a bai wa hukumar zabe maizaman kanta ikon gudanar da zabukan.
Irin wannan tabka magudin da dagewar da gwamnonin jihohin suke yi, na sai ‘yan takarar jam’iyyunsu sun lashe zabubbukan, ba zai sakarwa da shugabanninta mara ba don yiwa al’umomin su aiki, kamar yadda ya kamata ba.
Abin takaici ne, sai da goyon bayan gwamna ne, kawai dankarar kujerrar shugaban karamar hukuma ko kuma ta Kansila zai iya lashe zabe tare da amincewar wasu daga cikin jiga-jigan shugabannin jim’iyya mai ci.
Bugu da kari kuma, akasarin Kansilolin da suka lashe zabe, idan shugaban karamar hukumar ya aikata laifin da ya cancanci a tsaige shi, ba su da wani ikon iya tsige shi.
Duk wani darasin da aka koya na bai wa hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohin kasar nan ragamar gudanar da zabubbukan, hakan na ci gaba da nuna cewa, har yanzu wadanda aka zaba a matsayin shugagabannin kanannan hukumomin, na ci gaba da kasancewa ‘yan amshin Shata ne, wato za su ci gaba da kasancewa ne a karkashin ikon gwamnonin saboda tsayuwar da suka yi tsayin daka, wajen ganin shugabannin, sun lashe zabubbukan, wanda kuma a dole ne, sai sun bi umarnin gwamnonin
Lamarin dai, babban abin kunya ne a harkar dimokiradaiyyar kasar nan musamman ma ganin yadda gwamnonin, ke yin amfani da hukumomin gudanar da zabubbukan jihohinsu, don su tabka magudin zabe, wanda kuma haka ne ke nunawa a zahiri cewar, zabubbukan tamkarwata shiririta ce kawai.