El-Mansur Abubakar" />

Zaben NUJ A Gombe:  Wanne Dan Takara Ne Zai Cire Wa ’Yan Jarida Kitse Daga Wuta

Shirye-shiryen zaben kungiyar yan jarida ta kasa reshen jihar Gombe Nigeria Union of Journalist (NUJ) ya kammala inda za a gudanar da zaben a ranar Alhamis 26 ga watan Afirilu na wannan shekarar a babban dakin taron Sakatariyar kungiyar kwadago na Labour house dake unguwar Abuja Kwatas a fadar jihar.

LEADERSHIP A Yau Litinin ta tattauna da mutane uku da suka tsayawa takarar kujerar shugabancin kungiyar.

Sa’idu Bappah Malala, yana daga cikin yan takarar a hirarsa da wakilin mu ya bayyana manufofin sa na tsayawa takarar.

Ko za bayyana mana kanka dan jama’a su san wane ne kai?

Suna na Sa’idu Bappah Malala, kuma na kasance dan jarida yau kimanin shekara 25 nayi gwagwarmaya sosai wajen ganin ci gaban kungiyar mu ta NUJ a mataki daban-daban a nan jihar Gombe na kuma rike mukamai da dama.

 

Me ya baka sha’awar fitowa takarar kujerar shugaban kungiyar?

Na kuduri aniyar tsayawa takarar shugabancin NUJ ne dan na inganta tare da farfado da hanyoyin shigar kudin kungiyar saboda bai kamata ace kungiyar kwararru wanda sune na hudu a jerin gwamnati ba ta da hanyar shigar kudi yadda ya kamata ba.

 

Bayan inganta harka shigar kudin kungiyar me kuma za ka sa a gaba?

Zan hada kai da wasu kungiyoyi ko kafafe don ganin ana tura yan jarida wurare daban daban dan samu horon da ya dace na cikin gida da kuma na sanin makamar aiki saboda za ka ga dan jarida ya jima yana aikin amma ba fannin jarida ya kararnta kaga irin sa yana bukatar a kara masa horo dan ya kara sanin wasu dabarun aiki.

 

Jihar Gombe ba ta da sakatariya wato cibiyar yan jarida  press centre kamar sauran jihohi ya za a yi ka sharewa yan jarida haushin rashin wannan sakatariyar?

Yanzu haka aikin ginin Sakatariyar ya kai kashi 90 cikin dari na kammalawa idan na zama shugaba zan karisa aikin na samar da kayayyakin aiki na zamani dan sauwakewa yan jarida aikin su na yau da kullum sannan zan samar da abubuwan more rayuwa da hanyoyin samar da kudin shiga a wajen kuma samar da Sakatariyar zai taimaka idan aka samu bakin yan jarida za su zauna a wajen kafin su sami gida dan akwai wajen kwana.

 

Ka ce za ka biyawa mambobin ku kudin rijistar shiga jami’a ko kwalejin aikin jarida ta ya ya zaka samu kudin?

Eh daga kudaden da za a samarwa kungiyar na kudin shiga za a dinga cirewa ana biya sannan sauran kuma a gudanar da wasu aikace-aikace na kungiyar.

 

Ba za a rasa wadanda suke ganin an take su ba ta wata hanya idan akayi zabe Allah ya baka nasara ya ya za kayi wajen ganin ka hada kai da su dan a tafi tare?

Idan na ci zabe zan kira su mu zauna da su mu ga yadda za ayi a magance matsalolin dan a tafi tare saboda ba dan son rai za muyi tafiyar ba dan ciyar da kungiyar gaba ne.

 

Buri Na Na Karasa Ayyukan Da Muka Fara Idan Na Ci Zabe

 -Yusuf Baji

Yusuf Ishak Baji, shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar da wa’adinsu ya kare  suka sauka shi ma ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar inda yace idan yaci zabe zai karisa ayyukan da muka faro ba’a karisa ba.

 

Mene ne burinka na neman zama shugaban na NUJ?

Da farko dai nayi shekara 3 a matsayin mataimakin shugaba kuma akwai ayyukan da muka fara  a lokacin mu ba mu samu damar karisawa ba idan naci zabe zan karisa su har ma na bullo da sababbi.

 

Kamar wadanne irin ayyuka ne kuma wane sababbi kake son bullowa da su?

Zan yi kokari naga an kammala aikin ginin sakatariyar yan jarida wanda yanzu aikin ya kai kashi 70 cikin dari zan samar da kayayyakin aiki na zamani a cikin su wanda idan aka samar da kayan aiki zai takaitawa dan jarida ya rage masa zuwa café dan yin aiki wanda a wani lokaci takura ne ga     dan jarida yaje café dan yin aiki saboda aikin yana son sirri.

 

Mene ne alfaharinka ga yan jaridar?

Abun alfahari na na daya dana biyu dana uku shi ne kare hakkin dan jarida kare hakin da jarida a kowannen mataki saboda a mafi yawan lokaci ana take hakkin dan jarida a ci masa mutunci, sannan zan yi kokarin ganin a kalla duk shekara na tura mutane biyu cibiyar samun horo ta FRCN da TB Collage dake Jos dan samun horo a bangaren da ba lailai a koya maka a lokacin da kake karatun aikin jarida ba musamman yadda ake tace murya da gyaran hoto mai Magana wato Bideo wanda koda kana daga gida zaka yi aikin ka ka tura ofis ta yanar gizo a cire ayi amfani da shi kamar yadda nima na halarci wannan kwas din.

 

Akwai tsarin inshorar lafiya da sai mutum ya mutu iyalan sa suke amfana da shi wane mataki za ka dauka don ganin idan mutum ya raunata zai ci gajiyar ba sai ya mutu ba?

Eh, idan na zama shugaba zan nemi jami’oin da suke kula da wannan tsarin inshorar dan mu zauna da su muga yadda za a canja tsarin domin a nan Gombe a lokacin mu iyalan wani ma’aikacin gidan Talabijin na Gombe Sa’idu Muhammad Malam Inna Koron giwa sun amfana da wannan shirin wanda yanzu akwai Muhammad Ibrahim Pantami wanda ya yi hatsari sama da shekara uku yana jinya muna ta kokarin muga yadda shima zai amfana.

 

Idan Aka Zabe Ni Zan Magance Rikicin Addini Da Kuma Kabilanci -Umaru Gelengu

Umaru Ma’aji Gelengu (Kawu) yace idan aka zabe shi ya zama shugaban NUJ na Gombe zai kawo karshen matsalar banbancin addini da kuma kabilanci a tsakanin yan jarida a jihar Gombe.

 

Mene ne ya sa kake takarar shugabancin NUJ?

Na fito takarar neman shugabancin kujerar NUJ ne domin akwai abubuwan da naga suna faruwa nake son na gyara wanda shugabanin da suka gabata basu mayar da hankali akai ba.

 

Kamar wadanne abubuwa ne haka?

Shugaban da ya sauka bai ja sauran yan majalisar sa dan a tafi tare a ciyar da kungiyar gaba ba kuma komai ake yi sauran zababbun basu san me yake faruwa ba kuma bayan suma zababbu ne komai ake yi shugaba shi kadai yake yi sannan ina son samarwa kungiyar mota dan gudanar da zirga-zirgan kungiyar wanda kungiyar ba ta da shi idan za aje taro sai anyi aron mota zan magance wannan matsalar.

 

Ina aka kwana kan batun samar da Sakatariyar yan jarida wanda ita ce ake burin samu a jihar?

Eh, haka ne muna da waje a gefen rukunin gidaje na shongo wanda gwamnati ta samar mana da fili ta fara ginawa har aikin ya kai wani mataki amma saboda  wasu matsaloli ba ta gamu ba kuma laifin shugaban mu ne ba laifin gwamnati ba idan aka zabe ni na zama shugaba zan hada kai da yan kwangila na cikin gida ko gwamnati don ganin an kammala ta.

 

Bayan wannan, mene ne za ka kara don sanya walwala a fuskar yan jarida a jihar Gombe?

Aikin jarida yana bukatar walwala  zan samar da hanyoyi na karawa abokan aiki na kwarin guiwa na sanya su walwala wanda zai sa su nishadi dan aikin jarida idan ba nishadi aikin bai yiwu wa.

 

Ganin ana samu ’yan jarida da basu da ilimin na’urar zamani ta ya ya za su mori gwamnatin ka idan ka ci zabe?

’Yan jarida da dama basu da ilimin kwamfuta zanyi kokari idan na zama shugaba na samar musu da mafita wajen tura su koyon aiki da kwamfutar saboda idan aka gama aikin sakatariyar mu ta NUJ za mu sa Internet da zai bai wa kowa damar aika labaransa cikin sauki.

 

Ana kukan rashin kudi a wasu lokuta ya za ayi ka shawo kan matsalar idan aka zabe ka?

Zan tsaya da kyau muyi aiki da ofishin babban akanta na jihar wajen ganin inda kudaden mu da ake cirewa ina suke shiga sannan zan bullo da hanyoyin da za su samarwa kungiyar hanyoyin shigar kudi sosai.

 

Daga karshe LEADERSHIP A Yau ta ji ta bakin sakataren kwamitin shirya zaben, Salisu Ibrahim Nagodi dan jin shirinsu dangane da zaben, inda ya ce, duk wani shiri ya kammala saura jiran ranar zabe.

Exit mobile version