Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanya ranar 20 ga watan Mayu 2024 a matsayin ranar karshe da jam’iyyun siyasa za su mika sunayen wadanda za su tsaya takarar Gwamnan Jihar Ondo.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar a lokacin gagarumin taro a shalkwatan hukumar da ke Abuja, wanda ya hada da shugabanni da jiga-jigan mambobin jam’iyyu.
- Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
Shugaban hukumar INEC, Farefesa Mahmood Yakubu ya kara jaddada muhimmancin ranar da za a rufe karbar sunayen ‘yan takarar da za su tsaya wa jam’iyyu takarar gwamnan Jihar Ondo.
“Ina kira ga daukacin jam’iyyun siyasa su tabbatar sun aika da ainihin sunayen ‘yan takaransu a daidai lokacin da aka ayyana na ranar karshe 20 ga watan Mayun 2024, a lokacin ne ma shafinmu na yanar gizo za a rufe”.
Taron dai shi ne na biyu a wannan shekarar ta 2024, wanda aka mayar da hankali a kan zabukan da za a yi a jihohi da suka hada da Ondo da Edo da aka tsara a watan Satumba.
Hukumar INEC dai tuni ta kammala buga sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakansu a zaben gwamnan Jihar Edo. Daga cikin wadanda suka halarci wannan muhimmin taro akwai shugaban jam’iyyan APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure da shugaban jam’iyyar SDP, Shehu Gabam.
Farfesaa Yakubu dai ya yi kira da a tabbata an bi dokokin da hukumar zabe ta tanadar, “Abu ne mai muhimmanci ga dukkanin jam’iyyun siyasa da za su shiga zaben da su tabbatar sun bi dukkanin dokoki da tsare-tsaren da hukumar zabe ta tanadar don tabbatar da cewa an yi zaben cikin lumana”
A daidai lokacin ke karasowa, jam’iyyun siyasa suna ta fadi tashin ganin sun cika ka’idojin da hukumar INEC ta shimfida musu.