Muhammad Shafi’u Saleh" />

Zaben Sabbin Shugabannin APC Na Adamawa Zai Fi Kowanne Inganci –Shugaban Riko

Majalisar

Biyo bayan sanar da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar APC a kasa baki daya, jam’iyyar ta ce zata gudanar da zaben sabbin shugabanni mafi inganci da zai gudana bisa gaskiya da adalci a Adamawa.

Shugaban rikon jam’iyyar a jihar Ibrahim Bilal, ya bayyana haka cikin wata takardar sanarwar manema labarai, ta ce zaben shugabannin jam’iyyar da zata gudanar zaifi kowani zaben jam’iyya adalci a jihar.

Ta ci gaba da cewa kofa a bude take a aikin rigistar sabbin mambobin jam’iyyar da ke gudana yanzu haka, ta ce hakan shi zai bada dama ga mambobin jam’iyyar su fito kwansu da kwarkwata domin zaben shugabannin da sukeso su shugabancesu.

“kofa a bude take ga kowani mambobin jam’iyya da su fito kwansu da kwarkwata su yi rigista domin zaben sabbin shugabannin da sukeson su shugabancesu a jam’iyya.

“muna jaddada kiranmu ga daukacin ya’yan jam’iyya da su fito su yi rigista, domin su zabe shugabannin da sukeso a ranar Asabar 5\5\2018 da 12 da kuma 19 da za su zabe shugabannin jam’iyyar na jiha” inji takardar.

Takardar sanarwar ta kuma shawarci magoya bayan jam’iyyar da su gudanar rigistar cikin kwanciyar hankali da lumana, ta ce  bai kamata wasu su yi amfani da wannan dama wajan haifar rigima da tashin hankali tsakanin ya’yan jam’iyyar ba.

“wannan dama ce da tsarin mulkin jam’iyya ya bamu na mu gudanar da rigista cikin kwanciyar hankali da lumana, bai kamata mu bari wasu su yi amfani da wannan daman wajan haifar da rigima ba” tace.

Sanarwar ta kuma jaddada goyon baya ga sake tsayawa takarar shugaba Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, a babban zaben 2019, ta kuma bukaci magoya jam’iyyar da su mara musu baya.

 

Exit mobile version