A yanzu haka dai kallo ya koma kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya za su zabi shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, sannan a ranar 11 ga Maris za a gudanar da zaben gwamnonin da na ‘yan majalisun jihohi, wadanda za su ci gaba da jagorantar al’umma har na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Hukumar INEC ita ce alkali na nasanar da zabin da ‘yan Nijeriya suka yi kan wannan zabe, wanda tuni ta sha ikirarin gudanar da sahihin zabe da zai kasance karbabbe a wurin ‘yan Nijeriya da su kansu ‘yan takarar.
- Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa abin kunyar da ya faru a 2019 da aka dage zabe da mako guda a ranar jajibirin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya ba zai sake maimaita kansa ba bayan shekaru hudu.
Domin ganin zaben ya tafi kan yadda aka tsara, a watan Disamba da ta gabata, INEC ta rattaba hannu kan yarjejeniya tare da shugabannin kungiyar masu motocin haya ta Nijeriya (NARTO) da kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) da kuma kungiyar ma’aikatan ruwa ta kasa (MWUN) domin saukaka ingantacciyar hanyar isar da kayayyakin zabe cikin nasara.
A wurin wani taron yarjejeniyar, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa hukumarsa za ta bukaci motoci 100,000 da kwale-kwale kimanin 4,200 domin gudanar da harkokin zaben 2023.
“Mun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a yau da kungiyoyin sufuri na masu motocin haya da na ruwa, wanda yake nuni ne ga yunkurinmu na aiwatar da muhimman shawarwari kan zabe domin inganta harkokin zabenmu a 2023.
“Zaben 2023, ya kunshi tura ma’aikata sama da miliyan daya a fadin kasar nan baki daya tare da dimbin kayayyakin zabe a cikin makonni biyu daga ofisoshinmu na jihohi da ke kananan hukumoni 774 da mazabu 8,809 da rumfunan zabe 176,846 a fadin kasarmu Nijeriya. Domin haka, muna bukatar motoci 100,000 da kwale-kwale guda 4,200 wadanda za su kasance da sojojin ruwa,” in ji shugaban INEC.
Ya kuma tabbatar wa masu kada kuri’a cewa ma’aikatansa da kayayyakin zabe za su isa rumfunan zabe da wuri a ranakun zabe.
Domin gwada ingancin na’urar tantance masu kada kuri’a (BBAS), hukumar ta gudanar da gwajin tantance masu zabe a rumfunan zabe guda 436 da aka kebe a fadin kasar nan a farkon watan da ya gabata.
BBAS wata na’ura ce ta fasaha da za a yi amfani da ita wajen tantance masu zabe da daukar zanen yatsu na masu jefa kuri’a da kuma fuska kafin kada kuri’a. Haka kuma na’urar ce da ake amfani da ita don daukar hotunan takardar sakamakon zabe da saka hotunan sakamakon zaben a intanet.
Da yake zantawa da manema labarai jam kadan bayan ya ziyarci wasu jami’ai gwajin da aka nada a Abuja, Farfesa Yakubu ya ce an gudanar da wannan gwajin ne domin kawar da fargabar ‘yan Nijeriya, musamman wadanda suka nuna rashin jin dadinsu game da ingancin na’urar, wanda aka yi hakan domin cire shakku wajen gudanar da sahihin zabe.
“Tun da farko dai, abin da muke son cimmawa shi ne, mu kara gwada ingancin na’urorin da za mu tura a ranar zabe.
“Mun gamsu da gwaje-gwajen da aka yi a ofisoshinmu, amma muna bukatar mu kara gwada na’urorin kafin mu kai su filin zabe.
“Tun da yake cewa wannan shi ne karo na farko da za mu tura na’urori filin zabe a kasa baki daya, don haka mun yi gwaji a rumfunan zabe 436 da ke fadin kasar nan, bisa la’akari da daukan kananan hukumomi guda biyu daga kowacce gunduma da kuma rumfuna zabe hudu a kowacce karamar hukuma, wanda jimillar rumfanan zabe suka zama 16 a kowacce jiha, bisa ga wuraren da muka tura na’urorin.”
Ya kara da cewa idan aka samu rashin aikin ga wata na’ura ta BBAS a ranakun zabe, hukumar ta tanadi abubuwan da suka dace na bin wata hanya.
“A rumfunan zabe guda biyu da aka ziyarta kawo yanzu, babu wani rahoto na gazawa, saboda na’urorin suna gudanar da aiki yadda ya kamata.
“Kuma wannan shi ne rahoton da muke samu ya zuwa yanzu a fadin kasar nan, amma mun kuma yi shirye-shirye na gaggawa kamar yadda za mu yi a ranar zabe, cewa akwai na’urorin da aka tanada da za a iya amfani da su idan har aka samu matsala.
“Za mu iya gyara na’urar da ta ki yin aiki. Amma zuwa yanzu babu wata matsala, domin kuwa suna aiki yadda ya kamata. Babu abin da ya faru, babu gazawa kuma muna fata tare da addu’a su dore a haka wajen yin aiki da kyau a ranar 25 ga Fabrairu da ranar 11 ga Maris.”
Jimillar Yawan Masu Zabe A 2023
A zaman da aka yi a watan Janairun da ya gabata tare da shugabannin jam’iyyun siyasa 18, wanda ya gudana a shalkwatan hukumar INEC, shugaban INEC ya bayyana yawan adadin masu kada kuri’a a zaben 2023 guda 93,469,008.
Adadin ya nuna cewa Jihar Legas na da masu ragistan zabe 7, 060,195 wacce take kan gaba, sai Jihar Kano mai 5,921,370, Kaduna da Jihar Ribas na da 4,335,208 da 3,537,190, bi da bi. Jihar Ekiti ce ke da mafi karancin masu kada kuri’a da 502,251.
Bugu da kari, yankin arewa maso yamma ce ta fi yawan masu jefa kuria da mutum 22,255,562, sai kuma yankin kudu maso yamma mai mutum 17,958,966.
Adadin wadanda suka cancanci kada kuri’a ya nuna cewa maza sun kasance kashi 52.5, yayin da mata ke da kashi 47.5 na yawan adadin.
Da yake karin haske kan yadda hukumarsa ta kai ga wannan adadi, shugaban INEC ya bayyana cewa biyo bayan ci gaba da yin rajistar masu zabe aka samu karin masu jafa kuri’a 9,518,188, wanda a 2019 ake da 84,004,084. An cire jimillar 53,264 biyo bayan rashin bin ka’idojin rajista da hukumar ta shimfida.
Ya ce, “Idan za ku iya tunawa a zaben 2019, Nijeriya na da yawan masu kada kuri’a guda 84,004,084. Bayan tsaftace bayanai da aka yi tare da ci gaba da rajistar masu kada kuri’a na karshe a tsakanin watan Yunin 2021 zuwa Yulin 2022, an kara sabbin masu kada kuri’a 9,518,188, wanda aka samu jimallar masu jefa kuri’a na farkon rajistan guda 93,522,272, wanda aka gabatar wa ‘yan Nijeriya kamar yadda doka ta tanada.
“A karshe dai sakamakon rashin amincewar ‘yan kasa, hukumar ta samu 53,264 kan yawaitar wadanda ba su cancanta ba a cikin rajista ta hanyar shekaru, dan kasa ko kuma mutuwa. An tantance wadannan sunaye kuma an cire su daga rajistar zaben.
Bincike ya nuna cewa akwai adadin katunan zabe da dimbin yawa wadannan ba a amsa ba har zuwa lokacin da amsa ya kare da hukumar zabe ta saka.
Jam’iyyun siyasa da wasu kungiyoyin fararen huda na ci gaba da kira ga hukumar zabe ta bai wa ‘yan Nijeriya katinan zabe da ba a karba ba.
Da aka tambaye shi kan yaushe hukumar za ta bai wa ‘yan Nijeriya yawan adadin katin da ba a karba ba, Kakakin hukumar INEC, Mista Festus Okoye ya ce shugaban hukumar ne kadai zai iya yanke hukunci kan wannan.
Ya ce, “Duk masu kada kuri’a da suka yi rajista sun karbi katin zabensu, kuma hukumar ta bukaci dukkan kwamishinonin zabe su tattara alkaluman katin zabe da aka amsa da kuma wanda ba a karba ba.
“Hukumar za ta fitar da alkaluman katin zabe da aka amsa tare da ajiye wadanda ba a karba ba a Babbab Bankin Nijeriya (CBN). Za a sake su ne idan aka kammala zabe lokacin da aka sake fara yin rajistar masu zabe.”
Jam’iyyar mai mulki ta APC ta kammala yakin neman zabenta na shugaban kasa a Jihar Legas ranar Talata, wanda dimbin bagoya bayan suka yi tururuwa ga Asiwaju Bola Ahmad Tinubu kafin fara jefa kuri’a na zaben shugaban kasa a ranar Asabar.
A ranar kammala gangamin na APC a Jihar Legas, jam’iyyar ta nuna kokarinta ta ci gaba da darewa kan madafun iko a 2023.
Tun bayan kaddamar da yakin neman zaben a ranar 28 ga Satumbae 2022, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bole Tinubu ya zagaya kasar nan baki daya yana neman goyon baya da kuri’un ‘yan Nijeriya da suka cancanci kada kuri’a.
Tsohon gwamnan Jihar Legas ya bayyana cewa zama shugaban kasa nan shi ne babban burinsa na tsawon rayuwarsa, wanda ya gana da masu ruwa da tsaki domin cimma burinsa.
Idan za a iya tunawa, a yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma shirin aiwatar da dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar a watan Oktoban 2022 a Abuja, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin jagorantar yakin neman zaben na jam’iyyar APC.
Tun da farko dai ba a ji komai daga bakin shugaban kasan ba dangane da jajircewarsa na ganin jam’iyyar ta samu nasara. Duk da tabbacin da ya bayar na cewa zai jagoranci yakin neman zaben, ya ki nuna sha’awarsa sosai wanda hakan ya haifar da rade-radin cewa Buhari ba ya tare da Tinubu wajen samun shugabancin Nijeriya.
A matsayinsa na shugaban jam’iyyar, da an yi tsammanin Buhari ya zagaya jihohi 36 tare da Tinubu indai babu komi a tsakaninsu, domin ya mayar masa da abin da ya yi a zaben 2015. Amma hakan bai kasance ba.
Sai dai bayan an yi ta jan kafa, daga baya kwamitin yakin neman zaben APC ya fitar da sanarwa ta bakin kakakinsa, Festus Keyamo cewa, Buhari zai jagoranci yakin neman zaben Tinubu a jihohi 10 da suka hada da Adamawa, Yobe, Sakkwato, Kwara, Ogun, Kuros Ribas, Nasarawa, Katsina, Imo da kuma na karshe a Jihar Legas.
A lokacin yakin neman zaben jam’iyyar a Damaturu da ke Jihar Yobe, Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Tinubu zai ci gaba da gina kasa kamar yadda ya fara. Ya ce dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar shi ne mutumin da zai iya ci gaba da aikin sake gina Nijeriya da ya faro sama da shekaru bakwai da suka gabata.
“Na rako Asiwaju nan ne domin in ce muku ku zabi shi ya ci gaba daga ayyukan da na fara na sake gina Nijeriya,” in ji shi.
Dalilin da ya sa jam’iyyar APC ke neman ganin Buhari ya hau jirgin yakin neman zabenta domin ya kasance abin fahimta. Tun a shekarar 2003 da Buhari ya fara takarar shugaban kasa, a kowani lokaci yana samun sama da kuri’u miliyan 10, in ban da a 2007 wanda ya samu sama da kuri’u miliyan shida. Bisa la’akari da ganin cewa Buhari yana da dimbin masoya a yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas wanda ana tsammanin zai kasance nasara ga Tinubu.
Masu sharhin al’amurar siyasa suna ganin cewa wasu ‘yan Nijeriya sun sauka daga goyon bayan jam’iyyar APC bisa yadda gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Buhari ta kawo wasu sauye-sauye kan daina amfani da tsaffin takartun kudade na naira 1,000, 500 da kuma 200. Sai dai daga baya Buhari ya amince a ci gaba da amfani da naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu, wanda ake ganin jam’iyyar ta rasa magoya baya masu dimbin yawa.
A bin bakin ciki, yanzu mutane suna kwana a jefen na’urar cire kudi na ATM, domin cire kudi daga bankuna. Yayin da CBN ya umurci bankuna da su biya a kan tebur, hakan bai taimaka ba saboda an takaita ‘yan Nijeriya ta fuskar kudaden da za su iya cirewa. Wasu bankuna suna biyan naira 1,000 a kan kanta.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta sauya fasalin naira ne a daidai lokacin zabe, saboda kudaden da ‘yan siyasa suka sata wajen yin amfani da su domin siyan kuri’a.
Ko shakka babu wannan mataki ya yi matukar kawo wa jam’iyyar APC bakin jini wanda wasu gwamnonin arewa na jam’iyyar suka raba gari da gwamnatin tarayya.
A bangare daya kuawa, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kammala yakin neman zaben shugaban kasanta ne a Jihar Adamawa. Magoya bayan jam’iyyar tare da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da gwamnoni da ‘yan majalisan tarayya sun yi dafifi a wurin kammala yakin neman zaben shugaban kasa na PDP.
A yanzu haka, jam’iyyar PDP ta gudanar da gangamin yakin neman zabenta na shugaban kasa a dukkan jihohi 35 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, domin kira ga ‘yan Nijeriya su zabi jam’iyyar a 2023.
Sai dai jam’iyyar ta kasa gudanar da gangamin yakin neman shugaban kasa a Jihar Ribas.
A ranar Talata da ta gabata, jam’iyyar ta soke taron yakin neman zabenta da ta shirya a Jihar Ribas, saboda farmakin da aka kai wa magoya bayanta a jihar.
Jam’iyyar PDP na fama da rarrabuwar kawuna bayan zaben fid da gwani da Atiku Abubakar ya samu nasara a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Rikicin ya kai ga kafa kungiyar G5 na gwamnoni guda biyar karkashin jagorancin gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Wike da takwarorinsa ciki har da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom da gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu da kuma gwamnan Jihae Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi, wanda suka ware kansu daga yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, saboda kiraye-kiraye kan sai shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa.
Kiraye-kiraye sai Ayu ya sauka daga mukaminsa, a cewar fusatattun gwamnonin sun dogara ne a kan cewa dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyyar bai kamata su fito daga yankin arewa ba.
Ana ganin wannan rikicin na cikin gida na iya tasirin ga rashin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023.
Sai dai a wannan yakin neman zabe da jam’iyyun, an samu kalamun batanci da zage-zage a wurin kamfen duk da rattaba hannu da ‘yan takarar suka yi karkashin jagorancin kwamitin zaman lafiya da tsohon shugaban kasa, Abdussalam Abubakar yake jagoranta har karo biyu.
Haka kuma a wannan mako, hukumar INEC ta gayyaci ‘yan takarar shugaban kasa domin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya lokacin gudanar da zabe.
Rashin Tsaro Na Iya Hana Mutum Miliyan 10.90 Jefa Kuri’a A Yankin Kudu Maso Gabas
Karuwar kai farmaki kan kayayyakin gwamnati, musamman ma a ofisoshin INEC a yankin kudu maso gabas da ‘yan ta’adda ke kai wa na iya hana mutum miliyan 10.90 kada kuri’a a zaben 2023, wanda masana harkokin tsaro da kungiyoyin fararen huda da mazauna yankin suka yi gargadi.
A cewar hukumar INEC, akwai jimillar mutane 93, 469, 008 da za su kada kuri’a a zaben 2023. Jihohin biyar na kudu maso gabas wadanda suka hada da Abiya, Anambra, Ebonyi, Inugu da kuma Imo suna da masu rajistar zabe 10,907, 606.
Wani bincike ya tabbatar da cewa har zuwa yanzu akwai miliyoyin katunan zabe a wadannan yankuna da ba a karba ba sakamakon rashin tsaro wanda suka haifar da kai farmaki ofisoshin INEC da wasu ofisoshin ‘yansanda.
Yayin da ake yawan danganta wadannan hare-hare da ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, kakakin kungiyar fafatukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Simon Ekpa, ya yi ikirarin cewa ba za a gudanar da zabe a wadannan jihohi ba har sai an cika musu bukatocinsu.
A watan Disambar 2022, hukumar INEC ta bayyana cewa ta fuskanci hare-hare har sau 50 a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022. Fiye da kashi 70 na hare-haren sun faru ne a cibiyoyinta na kudu maso gaba da kudu masu kudu.
A daidai lokacin da ake kiraye-kiraye na inganta harkokin tsaro a yankin, an bukaci gwamnati kar ta yi amfani da karfin soja wajen gudanar da zabe a jihohin, domin yin hakan na iya kashe wa masu zabe kwarin gwiwa.
Ana ganin ya kamata jami’an tsaro su samu amincewa daga wurin jama’a ta hanyar fatattakar masu aikata laifuka a cikin al’umma.
Akwai masu ra’ayin cewa dole ne jami’an tsaro su yi hadin gwiwa da shugabannin al’umma ta hanyar inganta tsaro a yankunan.
Duk da irin kalubalen da hukumar INEC take fuskanta, a yanzu haka dai kanno ya kamo wurinta na gudanar da zabe a kowane sashi da ke Nijeriya a ranar Asabar.